Masu sharhi kan lamuran tsaro a Nijeriya sun soma tsokaci game da matakan da rundunar 'yan sandan kasar ke dauka na hukunta jami'anta da aka samu da laifin cin zarafin jama'a.
A baya-bayan nan rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta dauki matakai da suka hada da kora da rage mukami da makamantansu kan wasu jami’anta da aka samu da musguna wa jama'a.
Ranar Talatar da ta gabata rundunar ‘yan sandan ta rage girma ga wani jami’inta Insifekta Adejoh Siaka zuwa mukamin sajan.
Ta yi haka ne bayan an gan shi a wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta yana cin zarafin wani mutum.
Kazalika rundunar ta sallami ‘yan sanda uku daga aiki, wadanda ke bai wa fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara kariya.
An sallame su ne kan harbi a iska da suka rinka yi a lokacin da suke rakiya ga mawakin, lamarin da rundunar ‘yan sandan ta yi tir da shi da kuma cewa “abin kunya” ne ga aikin dan sanda.
"Irin wadannan matakai suna iya sauya yadda aikin dan sanda ke gudana a Nijeriya ganin cewa duk wadanda za su shiga wannan aiki sun san ba irin tsari na da ba ne inda za ka zo ka ci karenka ba babbaka."
A bara an ga yadda hukumar ta sallami wani jami’inta a Jihar Delta da ke kudancin Nijeriya mai suna Ubi Ebri kan zargin kashe wani matashi mai shekara 26.
Ya kashe matashin ne kan zargin kin ba shi cin hancin naira 100.
Bayan binciken da ‘yan sandan kasar suka yi, sai aka sallami jami’in sannan aka kama shi.
A 2020 ‘yan Nijeriya sun yi bore kan zargin da suke yi wa ‘yan sanda na cin zarafinsu ba tare da hukunci ba, lamarin da ya jawo har aka rushe rundunar da ke yaki da fashi da makami ta kasar wato, Sars.
Masu zanga-zangar sun yi ta zargin cewa akwai korafe-korafe da dama da aka gabatar kan wasu ‘yan sanda amma babu abin da aka yi.
Sai dai cikin alwashin da rundunar ‘yan sandan kasar ta sha bayan zanga-zangar da korafe-korafen, har da kara inganta aikinta da kuma hukunta duk wani jami’inta da ta samu da hannu a cin zarafin wani bil adama.
Jagoranci
Masana na ganin irin wadannan matakai za su inganta aikin dan sanda da kuma kimarsa a idanun 'yan Nijeriya.
Malam Kabiru Adamu, mai sharhi kan tsaro a Nijeriya, ya bayyana cewa da alamu irin wadannan matakan ba sa rasa nasaba da yanayin jagorancin ita kanta rundunar ‘yan sandan kasar.
“Tun da shi wannan babban sufeton ‘yan sandan ya hau muka ga ya dan yi kokari wajen daukar matakai na horar da jami’an ‘yan sanda wadanda ake tuhuma da irin wadannan laifuka,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Ya bayyana cewa yawanci idan irin wadannan batutuwa suka fito da suka hada da cin zarafin dan adam ko suka saba wa doka, yakan kaddamar da bincike kuma a cikin dan karamin lokaci ana hukunta wadanda ake tuhuma.
“Wannan mai yiwuwa yana da nasaba da zanga-zangar Endsars, idan ba mu manta ba abin da ya kawo wannan zanga-zangar, irin wannan cin zarafin ne da aka yi,” in ji Malam Kabiru.
Ya ce wannan zanga-zanga ta kasance barazana ga shugaban kasa da kuma shi kansa shugaban ‘yan sanda na lokacin.
“Mai yiwuwa wannan ne ya sa shi shugaban ‘yan sandan na yanzu ya soma hannunka mai sanda ya fara daukar wadannan matakan," in ji shi.
Sauyi ga aikin dan sanda
Manjo Yahaya Shinko, wani mai sharhi kan tsaro a Nijeriya, ya shaida wa TRT Afrika cewa wadannan matakan da rundunar ‘yan sanda ke dauka za su kawo sauyi da kuma inganta aikin a Nijeriya.
“Irin wadannan matakai suna iya sauya yadda aikin dan sanda ke gudana a Nijeriya ganin cewa duk wadanda za su shiga wannan aiki sun san ba irin tsari na da ba ne inda za ka zo ka ci karenka ba babbaka,” in ji shi.
A cewarsa, hakan zai zama darasi ga ‘yan sandan da ke ganin za su iya yin abin da suka so ba tare da an dauki wani mataki ba, haka kuma ya ce ga masu son shiga aikin dan sanda su ma wannan zai zama darasi a gare su.
“A yanzu tun daga lokacin da mutum zai shiga wannan aiki ya san akwai wasu irin kalubale da ke jiransa wadanda ya kasance dolensa ne ya bayar da kansa shi ma ya yi biyayya ga doka.
“Domin idan bai yi biyayya ba, abin da ya samu wadannan da ya ga ana hukuntawa shi ma haka na iya samun sa. Hakan kamar an tauna tsakuwa ce domin aya ta ji tsoro,” in ji Manjo Shinko.
Ya kuma ce wurin daukar ma’aikatan ‘yan sanda dole abin zai sauya ba kamar yadda ake yi a baya ba.
‘Kara wa talakan Nijeriya kwarin gwiwa’
A cewar Aliyu Gora, wani dan jarida a Nijeriya, “talaka ya soma cire tsammani kan cewa za a rinka kwato masa hakkinsa daga zaluncin da wasu daidaikun jami’an ‘yan sanda ke yi”.
Ya bayyana wa TRT Afrika cewa akwai wasu jami’an ‘yan sanda da suke ganin a baya ba sa tabuwa, amma a halin yanzu suna hannu.
“A ra’ayina, irin wannan matakin abin a yaba ne kuma hakan kara wa talakan Nijeriya kwarin gwiwa ne domin ya yarda da cewa ashe har su jami’an ‘yan sandan ana iya hukunta su,” in ji Gora.
“An yi lokacin da dan Nijeriya ne kawai zai ga dan sanda ya ga kamar ya ga makiyinsa a maimakon ya ji dadi kan cewa watakila ya ga aboki, wanda yake ganin idan yana wurin babu wani abin da zai iya faruwa da shi.
Shi ma Malam Kabiru Adamu yana da makamancin wannan ra’ayi na Aliyu Gora. “Ba shakka idan aka ci gaba, haka zai taimaka wurin rage gibin da ake da shi na rashin yarda da ake da ita tsakanin ‘yan kasa da hukumar ‘yan sanda,” in ji Kabiru Adamu.