Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce ta’addanci “babbar masifa ce da aka shigo da ita” kuma ya zama wata annoba ga nahiyar Afirka.
A jawabin da ya gabatar a wajen buɗe wani babban taron yaƙi da ta'addanci na kasashen Afrika na kwanaki biyu a Abuja babban birnin kasar, Tinubu ya bayyana cewa ana kashe biliyoyin kuɗaɗe da suka kamata a yi amfani da su wajen kula da lafiya da ilimi da samar da ababen more rayuwa a nahiyar a duk shekara, duk a wajen sayen makaman yaƙi da 'yan ta'adda.
"Dole ne mu yi magana a kan wannan mummunan bala'i da aka shigo da shi wanda yake son karya mu, mu ga cewa lallai ba mu bari hakan ya faru ba," in ji shi.
Ya ce, 'yan ta'adda na neman ƙarfafa son zuciya a nahiyar da kuma kawar da mulkin dimokuraɗiyya da kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da harkokin tattalin arziki na ƙasashe da dama.
Ya bukaci shugabannin ƙasashen Afirka da su magance talauci da inganta ilimi ba ya ga salon yaƙi da ta'addanci da sojoji ke yi.
Shugaban na Nijeriya ya kuma buƙaci takwarorinsa na yankin da su mayar da hankali kan haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba da ake amfani da su wajen samun kuɗaɗen ta'addanci.
"Wadɗanda suke tunanin hakar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba ba ta da wata alaƙa da tallafa wa ta'addanci to sun yi kuskure sosai. Ƙasashen duniya suna da alhakin halin taimakawa a wannan harka saboda da kudaden waje ake hada-hadar ba kudin Afirka ba, wadanda su ke haifar da wadannan miyagun ayyuka," ya ce.
Mataimakin Sakatare Janar na ofishin yaki da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya Vladimir Voronkov, ya ce taron na da nufin magance matsalar ta'addanci da ke ƙara ƙamari a nahiyar.
Ya ce kungiyoyin 'yan ta'adda irinsu Daesh/ISIS da Al-Qaida da masu alaƙa da su suna matsawa kudu zuwa mashigin tekun Guinea da ke kudanci da tsakiyar Afirka bayan sun kafu a yankin Sahel, inda ya yi kira da a ƙara ba da hadin kai tsakanin shugabannin nahiyar domin dakile yaduwar ta'addanci.
Shawarwarin Tinubu
Shugaban na Nijeriya ya bayar da muhimman shawarwari a wajen taron ƙolin na yaƙi da ta'addanci na kasashen Afrika, kamar:
1. Samar da wata cibiya ta tsakiya ga kasashen Afirka don musayar bayanai da hada kai don yaki da ta'addanci
2. Magance tushen ta'addanci, tare da talauci da rashin daidaito
3. Yanke hanyoyin samar da kudade don ta'addanci, kamar haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da kuma biyan kudin fansa
4. Haɓaka ƙarfi da ingancin ƙungiyoyin da ke yaƙi da ta'addanci
5. Ƙirƙirar dakaru na musamman don mayar da martani cikin gaggawa game da ta'addanci da sauran barazanar tsaro
6. Kafa kwamitin da zai hada kai da samar da jagoranci kan yaki da ta'addanci
7. Ƙarfafa ƙarfin yaƙi da ta'addanci na daidaikun ƙasashe
8. Dakatar da yaduwar makamai masu hadari a fadin Afirka
9. A dauki kwakkwaran mataki don magance barazanar tsaro a nahiyar.
Taron mai taken karfafa hadin gwiwa tsakanin shiyya da kafa cibiyoyin yaki da ta'addanci a nahiyar Afirka, ya samu halartar mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed da shugabannin ƙasashe da gwamnatocin kasashen Afirka da dama da kuma manyan jami'an MDD.