A ranar Litinin, IGP ya yi kira da a ƙara ƙaimi don “magance matsalar masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka” a babban birnin kasar. Hoto: NPF

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ƙaddamar da wata runduna ta musamman mai suna SIS domin yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a fadin kasar, musamman a babban birnin tarayya, Abuja.

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun wanda ya kaddamar da rundunar a ranar Laraba ya ce ta ƙunshi ƙwararrun jami’an ‘yan sanda na musamman, da ingantattun kayan aiki da kuma na’urorin tafi da gidanka.

Ya kuma ce rundunar na da ƙarfin shiga tsakani da gaggawa da kuma daƙile munanan matsalolin tsaro, kamar wadanda a halin yanzu ke barazana ga jami’an tsaro a kewayen birnin tarayya da kuma haifar da firgici gaba ɗaya.

Wannan abu na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka sace wasu 'yan mata shida ƴan gida ɗaya, inda daga baya masu garkuwan suka kashe ɗaya daga cikinsu, tare da buƙatar kudin fansa mai matuƙar yawa don kubutar da sauran.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce da Allah wadai a fadin ƙasar, inda mutane ke nuna farabarsu kan rashin tsaron da ke yin barazana a kowacce rana.

A ranar Litinin, IGP ya yi kira da a ƙara ƙaimi don “magance matsalar masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka” a babban birnin kasar.

Sai dai Sufeto Janar na ƴan sandan ya ce; “Wannan shirin ba wai kawai an ƙirƙire shi ne bisa larura ba, sai don hangen nesa da tsare-tsare da himma don inganta ingantaccen tsarin tsaro na babban birnin kasarmu.

“FCT ta kasance ginshikin aminci da misali na ingantaccen tsarin kula da tsaro a birane. Ko yaya, a cikin neman ƙwarwarmu, dole ne mu yi aiki da hankali wajen magance duk wata barazana. Don haka ya zama wajibi mu tinkari dukkan kalubale don kare rayuka da jin dadin 'yan kasarmu."

A yayin ƙaddamar da tawagar a Abuja, IGP Kayode Egbetokun ya ce tawagar ta haɗa da ƙwararrun jami'an ƴan sanda na tafi da gidanka, waɗanda ake sa ran za su ba da ɗauki cikin gaggawa kan taɓarɓarewar tsaro a babban birnin tarayya Abuja.

Da yake fayyace cewa rundunar za ta gudanar da ayyukan ‘yan sanda masu tarin yawa a cikin al’umma, Mista Egbetokun ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a sake samar da irin sabuwar runduna ta musamman da aka ƙaddamar ɗin a jihohi maƙwabta domin magance ƙalubalen rashin tsaro.

Reuters