Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a Somaliya ya ce ya soma gangamin aikin ba da allurar riga-kafin cutar polio a ƙasar.
Wannan yunƙuri na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar da ke haifar da kuturta da shanyewar wasu sassan jiki wadda a yanzu haka ta ɓulla a wasu ƙasashen kudancin Afirka.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ƙarshen mako, UNICEF ya ce, ya soma wani gangami na ba da allurar riga-kafin na tsawon kwanaki biyar, kuma ''ana sa ran yi wa yara sama miliyan 2.7 ƴan kasa da shekaru biyar allurar a gundumomi 80''.
A watan Yunin 2022, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ba da shawarar kai ɗauki ga wani sabon nau'in cutar shan inna da ta ɓulla take kuma yaɗuwa a yankin Kudancin Afirka.
A shekarar 2022 ne Somaliya ta fitar da rahotonta na ƙarshe kan ɓullar cutar shan inna (Polio) bayan da wasu yara biyar suka kamu da cutar.
Yaɗuwar cutar
Kazalika ƙasar Mozambique ta ayyana ɓarkewar cutar a ranar 17 ga Fabrairun 2022, inda maƙwabciyarta Malawi ta ba da rahoton samun wasu mutum tara da suka kamu da cutar a watan Agustan wannan shekarar.
Tun daga lokacin, cutar ta yaɗu zuwa ƙasar Botswana da Burundi da Rwanda da kuma Zambiya.
A watan Fabrairu, Zimbabwe ta ce, za a ba da allurar riga-kafin cutar Polia miliyan 4.2 ga yara ƴan kasa da shekaru 10 bayan da aka gano wani sabon nau'in cutar da ya ɓulla a yankin Sanyeti da ke tsakiyar ƙasar Zimbabwe.
Cutar wacce ke da saurin yaɗuwa, takan mamaye sassan jiki kuma takan haifar da kuturta da shanyewar jiki gaba daya cikin yan sa'o'i, a cewar WHO.
Kwayar cutar tana yaɗuwa daga mutum zuwa mutum musamman ta gurɓatattun hanyoyi marasa tsabta da najasa sannan ana iya kiyaye cutar ta hanyar yin riga-kafi.