"Hare-haren sun yi matuƙar taimakawa wajen rage ƙarfin ƙungiyar a yankin," in ji rundunar sojin saman Nijeriyar. Hoto / Reuters

Dakarun tsaron Nijeriya sun kashe gomman masu tayar da ƙayar baya da suka haɗa da manyan kwamandojin ƙungiyar ISWAP, a yankin arewacin ƙasar, kamar yadda rundunar soji ta bayyana a ranar Talata.

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ce ta kai hare-haren sama a maɓoyar mayaƙan ƙungiyar a kusa da Tafkin Chadi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

ISWAP ita ce ƙungiyar da ta ɓalle daga Boko Haram. Ta daɗe tana ayyukan ta'addanci a Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, inda ta kashe dubban fararen hula da jami'an tsaro, tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.

"Hare-haren sun yi matuƙar taimakawa wajen rage ƙarfin ƙungiyar a yankin," kamar yadda rundunar sojin saman Nijeriya ta faɗa a cikin wata sanarwa.

An kashe ƴan ta'adda

An kai hare-haren a ƙauyen Kolleram ne tun a ranar Asabar, amma ba a sanar wa al'umma ba sai a ranar Talata.

Aƙalla masu tayar da ƙayar baya 30 aka kashe, ciki har da manyan kwamandojin ƙungiyar, Ali Dawud da Bakura Fallujah da Mallam Ari, in ji rundunar sojin.

"Waɗannan hare-haren suna nuna irin muhimmin ci gaban da ake samu na yaƙi da ta'addanci a Nijeriya," a cewar sanarwar.

Hare-haren sun lalata wani muhimmin waje da ƙungiyar ke amfani da shi wajen ayyukan samar da abinci," sanarwar ta faɗa.

TRT Afrika
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince