Mohamed Bazoum ya yi zargin cewa sojojin sun ajiye shi cikin mawuyacin hali tun da suka yi masa juyin mulki ranar 26 ga watan Yuli./Hoto: Reuters.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun sha alwashin tuhumar hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum bisa laifin "cin amanar kasar."

Wata sanarwa da kakakin sojojin Amadou Abdramane ya karanta a gidan talabijin na kasar ranar Lahadi da maraice, ta ce za a tuhumi Bazoum da "babban laifi na cin amanar kasa da yin kafar-ungulu kan tsaron cikin gida da wajen Nijar."

Sanarwar ta kuma caccaki shugabannin kungiyar kasashen Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) bisa sanya takunkumai kan Jamhuriyar Nijar da barazanar yin amfani da karfin soji kan sojojin da suka kifar da gwamnatin dimokuradiyya ta Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.

Kungiyar ta Yammacin Afirka ta umarci dakarunta su kasance "cikin damara domin maido da tsarin mulki" a Nijar nan ba da jimawa ba ko da yake ta ce za ta ci gaba da bin hanyar diflomasiyya don warware rikicin.

Bazoum, mai shekara 63, da iyalansa suna tsare a gidansa na shugaban kasa da ke Yamai tun da aka yi masa juyin mulki, kuma kasashen duniya suna nuna fargabar kan mawuyacin halin da suke ciki.

Labari mai alaka: Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar 'sun ki' sakin iyalan Bazoum

Wani makusancinsa ya ce an kyale likitansa ya gana da shi.

"Bayan wannan ziyara, likitan bai bayyana cewa akwai wata matsala ba game da koshin lafiyar hambararren shugaban kasar da iyalansa," a cewar sojojin.

Sun ce takunkuman da aka kakaba wa Nijar sun sa mutane suna shan wahalar samun magunguna da abinci da wutar lantarki, kuma sun "karya doka sannan rashin imani da wulakanci ne".

'Diflomasiyya'

Wannan sanarwa na zuwa ne kwana guda bayan wasu fitattun Malaman addinin Musulunci na Nijeriya sun gana da jagoran masu juyin mulkin Janar Abdourahamane Tiani, wanda ya amince ya zauna kan tebirin sulhu da kungiyar ECOWAS.

Tiani "ya ce kofarsa a bude take domin yin tattaunawar diflomasiyya da samun hanyar warware matsalar cikin lumana", a cewar Sheikh Abdullahi Bala Lau, jagoran Malaman da suka gana da shi a Yamai.

Tiani "ya yi ikirarin cewa an yi juyin mulki ne da manufa mai kyau" kuma sojojin sun kifar da gwamnatin Nijar ne "domin hana yiwuwar wata barazana" da za ta iya shafar Nijeriya, a cewar sanarwar da Sheikh Bala Lau ya fitar.

AFP