Sojojin Nijar sun kwace kariyar diflomasiyya da jakadan Faransa yake da ita sannan suka umarci 'yan sanda su fitar da shi daga kasar.
A makon jiya ne sojojin, wadanda suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum, suka bai wa jakadan Faransa Sylvain Itte wa'adin awa 48 ya fitar daga kasar.
Wa'adin ya kare ranar 28 ga watan Agusta amma Itte ya ci gaba da zama a Yamai.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa ba ta amince da sojojin ba saboda ba ta halastacciyar hanya suka karbi mulki ba, yana mai cewa jakadansu zai ci gaba da zama a Nijar.
Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun katse lantarki da ruwa a ofishin jakadancin Faransa
Hasalima ya jaddada goyon bayansa ga hambararren Shugaba Mohamed Bazoum, wanda ya yaba wa saboda kin yarda ya yi murabus.
Wata wasika da Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijar ta fitar a wannan makon wadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya gani ranar Alhamis ta ce daga yanzu Itte "ba zai samu kariyar da ake ba shi ba a matsayin ma'aikacin diflomasiyya."
Wasikar ta ce an soke shaidar katin diflomasiyya da kuma biza na iyalansa.