Akasarin mutanen da ke zaune a karkara a Nijar sun dogara ne da tafiya ci-rani domin taimakon iyalinsu. / Hoto:Reuters

Sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun soke dokar da ta taimaka wurin rage kwararar ‘yan kasashen Yammacin Afirka zuwa Turai musamman mazauna karkara wadanda ke fama da matsin tattalin arziki da suka dade suna dogara da ci-rani.

An yi dokar ne a 2015 wadda ta haramta jigilar jama’a ta cikin Nijar ba bisa ka’ida ba don ratsawa ta Bahar Rum daga Afirka zuwa Turai.

Gwamnatocin kasashen Turai sun sha kokawa kan matsin lambar da suke fuskanta a cikin gida sakamakon kwararar ‘yan ci-rani daga Afirka.

Sojojin Nijar, wadanda suka yi juyin mulki a watan Yuli, sun soke dokar ne a ranar Asabar amma sun sanar da ita ranar Litinin da daddare a gidan talabijin.

Gwamnatin mulkin sojan tana sake nazarin alakarta da tsofaffin kawayenta na Kasashen Yamma wadanda suka yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar.

Ana ganin gwamnatin Nijar din ta dauki wannan matakin ne domin kara samun goyon baya a cikin gida.

Tasirin matakin

Adadin ‘yan ci-ranin da ke shiga ta cikin Nijar, wadda ita ce kasar da aka fi ratsawa da yada zango a tafiya zuwa Turai, ya ragu matuka a tsawon shekaru sakamakon wannan dokar. Sai dai a baya dokar ta sa iyalai da dama sun shiga wahala musamman wadanda ke kauyuka da garuruwan da ke kan hanya wadanda suka rika bayar da mafaka da abinci da sayar da kayayyakin mota ga wadanda ake zargi da safarar jama’a.

Sakamakon wannan doka da aka saka, Tarayyar Turai ta kaddamar da wata gidauniya ga Afirka a 2015 ta euro biliyan biyar, inda aka ware kudin domin kawar da matsalolin da ke tattare da ci-rani, sai dai da dama suna ganin wannan matakin bai isa ba.

Rashin aikin yi ya karu a birane irin su Agadez, wanda wuri ne da ya yi suna ga masu tafiya ta cikin Sahara.

TRT Afrika