Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun sanar da nada ministoci ashirin da daya a yunkurinsu na kara tabbatar da ikonsu a kasar.
Shugaban sojojin Janar Abdourahamane Tchiani ne ya bayyana haka a sanarwar da ya karanta a gidan talabijin na kasar ranar Laraba da daddare.
A cewarsa, sabon Firaiministan kasar Ali Mahaman Lamine Zeine ne zai jagoranci gwamnatin mai mambobi 21.
An bayar da mukaman ministan tsaro da na cikin gida ga janar-janar biyu na sabuwar rundunar zartarwar sojin kasar.
Sojojin sun dauki matakin ne a yayin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ke shirin yin taro a Abuja ranar Alhamis game da matakin da za ta dauka bayan karewar wa’adin da ta bai wa sojojin na mayar da Shugaba Mohamed Bazou kan mulki.
Kazalika sojojin sun zargi Faransa da sakin masu ikirarin jihadi da ke daure da kuma keta dokar da suka sanya ta rufe sararin samaniyar kasar.
Sun zargi Faransa “da yin gaban kanta wajen sakin masu ikirarin jihadi da aka daure” – wadanda suka dade suna kai hare-hare a kasar.
Daga nan ne masu ikirarin jihadin suka taru wuri guda inda suke shirin kai hare-hare "a wurare uku" da dakarun Nijar da Burkina Faso da Mali suke haduwa, a cewar wata sanarwa da shugabannin juyin mulki na the National Council for the Safeguard of the Homeland (CNSP) suka fitar ranar Laraba.
"Wasu abubuwa masu tayar da hankali suna faruwa a Nijar sakamakon halayyar dakarun Faransa da abokansu," in ji sanarwar.
Sanarwar ta yi kira ga jami’an tsaro su “kara kaimi wajen sanya ido a fadin kasar" da kuma ‘yan kasar "su ci gaba da lura" game da abubuwan da ka je su dawo.
Kazalika sojojin sun zargi Faransa da tura "jirgin soji" daga makwabciyar kasar Chadi zuwa sararin samaniyar Nijar ranar Laraba, inda ta keta dokar da kasar ta sanya ta haramta shiga sararin samaniyarta.
Mali ta dakatar da ba da biza ga 'yan kasar Faransa
A gefe guda, kasar Mali da ke da makwabtaka da Nijar ta dakatar da bayar da biza ga 'yan kasar Faransa.
Wannan mataki ya nuna karara yadda dangantaka ta tabarbare tsakanin kasar da tsohuwar uwar gijiyarta.
Ma'aikatar harkokin wajen Mali ta sanar da matakin da kasar ta dauka na dakatar da bayar da biza ga duk wani 'dan kasar Faransa har sai baba-ta-gani.
Ma'aikatar ta bayyana cewa matakin martani ne ga “abin mamakin” da ta ji daga kafafen yada labarai kan cewa ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ware Mali a matsayin "yankin da ba a shiga" bisa dalilan cewa kasar na fama da yawan “tashe-tashen hankula a yankunanta.”
A daya bangaren rahotonin sun yi nuni da cewa ita ma Faransa ta dakatar da bayar da biza tare da rufe cibiyar biza a ofishin jakadancinta da ke Bamako babban birnin kasar ta Mali.