Tchiani ya jagoranci sojojin Nijar wajen kifar da gwamnatin Bazoum: Hoto AA

Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta bukaci Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe da ya zama mai shiga tsakani don tattaunawa da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa ciki har da ECOWAS ta Yammacin Afirka, wadda ta saka musu takunkumai tun bayan juyin mulki.

Ministan Tsaro na Nijar Janaral Salifou Mody ya gana da Gnassingbe a babban birnin Lome na kasar Togo inda ya ce gwmanatin sojin na bukatar Togo ta zama garanto wajen tabbatar da ficewar sojojin Faransa daga yankin na Sahel.

Kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta kakaba wa Nijar tsauraran takunkuman sha'anin kudi tare a rufe iyakokinta na kasuwanci da Nijar, a kokarin neman dawo da kasar kan turbar dimokuradiyya.

Mody da ya bayyana takunkuman a matsayin "son zuciya", ya kuma ce Togo ce ta bayar da kofa ga Nijar don a tattauna, a lokacin da sauran wurare suka rufe kofar hakan.

Yunkurin diflomasiyya

Duk da cewa mamba ce ta ECOWAS, Togo ta dauki wasu matakai na diflomasiyya don ganin an tattauna da shugabannin sojin Nijar.

"Ba mu taɓa rufe kofar mu don kar abokanmu su shigo ba. Yana da muhimmanci mu tunawa ƙawayenmu cewa Nijar a bude take ko yaushe, duk da an yi tsarin da ya hana mu damar magana da abokanan huldarmu," Mody ya fada wa manema labarai bayan ganawar.

"Mun kuma bukaci Shugaban Kasar Jumhuriyar Togo da ya zama mai shiga tsakani, don samun damar tattaunawa da abokanan huldarmu daban-daban."

Tuni Faransa ta fara janye sojojinta 1,500 daga Nijar bayan gwamnatin juyin mulkin ta nemi da su tattara su bar kasarta, sakamakon kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 28 ga Yuli 2023.

'Ana ci gaba' da janye sojojin Faransa

Mody ya kuma ce ana ci gaba da janye sojojin yayin da ake shirya wasu kayan yakin sama na Faransa don tafiya.

Ya ce "Mun bukaci cewa Togo, kasa 'yar uwarmu, saboda gudunmowar da take ci gaba da ba mu, da ta zama garanton tabbatar da wannan janye wa ta sojojin Faransa. Janyewar na ci gaba ba tare da wata matsala ba."

Ministan harkokin wajen Togo Robert Dussey ya ce kasar ta shirya don taimakawa wajen tattaunar.

"Togo a shirye take ko yaushe wajen nuna adawa da ƙwatar mulki da ƙarfi, Togo na adawa da juyin mulki. Amma duba da yanayin da ƙasarku ke ciki, Togo na son taimaka muku don warware matsalar."

Shekaru uku na miƙa mulki ga farar hula

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinuba, shugaban ECOWAS na yanzu ya ce yana taka tsan-tsan kan Nijar ne saboda damuwa game da rayuwar hambararren shugaban Nijar Bazoum.

A yanzu dai, gwamnatin juyin mulki ta Nijar ta bukaci shekara uku kafin ta miƙa mulki ga farar hula, yayin da ECOWAS ta yi kira da a dawo da aiki da kundin tsarin mulki a kasar ba tare da bata lokaci ba. Amma Tinubu ya ce har yanzu ƙofofi a bude suke.

Nijar na yaƙi da 'yan ta'adda nau'i biyu - rikicin a ɓangaren kudu maso gabashinta da ya faro daga maƙwabciyarta Nijeriya, da kuma hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa a yammacin kasar da ke iyaka da Mali da Burkina Faso.

TRT Afrika