Abdourahmane Tiani ya ce ba zai amince da katsalandan daga kasashen waje ba./Hoto: Ofishin Shugaban Nijar

Sojojin Nijar sun amince da sharuddan mika mulki ga gwamnatin farar-hula, kuma za su gabatar da tsarinsu na yin haka ga kungiyar ECOWAS, a cewar wani jam'in diflomasiyyar kasar Togo wadda ke shiga tsakanin bangarorin biyu.

Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey ne ya bayyana haka ranar Alhamis a wata hira da gidan talbijin na Jamhuriyar Nijar.

Ya ce an cim ma yarjejeniya "game da lokaci da kuma tsare-tsaren" mika mulki a ganawarsu da Firaiministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine da ministan harkokin waje Bakary Yaou Sangare.

"Mun shirya gabatar da tsare-tsare... ga shugabannin kasashen da ke shiga tsakani da kuma Majalisar ECOWAS," in ji shi.

ECOWAS ta sanya wa Nijar jerin takunkumai ciki har da na rufe kan iyakokin mambobinta da katse lantarki da ake ba ta daga Nijeriya da kuma dakatar da kasar daga harkokin kudi na kungiyar, tun da akaThe bloc also decided that a committee made up of the presidents of Benin, Togo and Sierra Leone would lead negotiations with the Nigerien military leaders on the commitments to be implemented. kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Takunkumai masu tsauri

Takunkuman da aka sanya wa Nijar da kuma cire ta daga cikin harkokin kasashen duniya sun jefa ta cikin karin matsin tattalin arziki.

A watan Oktoba, shugabannin sojojin sun sanar da rage kashi 40 cikin dari na kasafin kudin kasar na 2023 "sakamakon takunkuman da kasashen duniya da na lardi suka sanya mana".

A taron ECOWAS na ranar Lahadin da ta gabata, shugabanninta sun gindaya wa sojojin Nijar sharudda kafin su cire musu takunkumai.

Sun nada kwamitin mutum uku na shugabannin kasashen Togo da Benin da Saliyo domin tattaunawa da sojojin Nijar da kuma bibiyar yadda za su cika wadannan sharuddan.

A baya dai, sojojin na Nijar sun ce za su iya kwashe shekara uku a kan mulki kafin su sauka.

A cewar kafar watsa labarai na Nijar, Tele Sahel, Dussey zai koma Yamai a watan Janairu tare da takwaran aikinsa na Saliyo Timothy Kabba.

Ranar Alhamis ECOWAS ta ce ta "dakatar da Nijar daga duk wasu hukumomi da ke d karfin iko" sai an "dawo da tsarin mulki"a kasar.

AFP