Rashin tsaro ya yi ƙamari a Mali a shekarar 2012 inda ya bazu zuwa Nijar da Burkina Faso. / Hoto: Reuters

Rundunar Sojin Mali a ranar Asabar ta sanar da cewa dakarunta sun kama wasu mutum biyu, inda ɗaya daga cikinsu jagora ne a wata ƙungiyar ta'addanci a yankin Sahel.

Rundunar sojin ta kuma sanar da cewa ta kashe mayaƙan ƙungiyar ta'addancin da dama a lokacin da ta kai wani samame a arewacin ƙasar.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta bayyana cewa ta kama "Mahamad Ould Erkehile wanda aka fi sani da Abu Rakia", da kuma "Abu Hash" wanda suka ce shi ne ke jagorantar ƙungiyar.

Sojojin na zarginsa da kitsa muggan hare-hare na zalunci a yankunan Menaka da Gao da ke arewa maso gabashin ƙasar, da kuma hare-hare kan sojojin ƙasar.

Yanke hulɗa da Faransa

Rashin tsaro ya yi ƙamari a Mali a shekarar 2012 inda ya bazu zuwa Nijar da Burkina Faso.

Shugabannin sojin ƙasar sun yanke hulɗa da Faransa wadda ita ce ta yi musu mulkin mallaka inda suka karkata zuwa ga Rasha.

AFP