Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun sanar da cewa za su bude iyakar kasar nan-take wadda aka rufe bayan juyin mulkin kasar.
Wani mai magana da yawun sojojin kasar ya sanar da wannan matakin a yayin wani jawabi da ya yi a ranar Asabar a gidan talabijin na kasar.
Ya ce sun yanke shawarar “bude iyakar kan tudu da ta ruwa da ta sama nan-take a ranar Asabar,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
A ranar Laraba ne wasu sojoji 12 suka fito a gidan talabijin na kasar jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben kasar inda suka sanar da hambarar da gwamnatin Ali Bongo da kuma rufe iyakokin kasar.
Labari mai alaka: Sojoji ba za su yi gaggawar gudanar da zabe a Gabon ba
Janar Brice Oligui Nguema, wanda shi ne shugaban sojin da ke kula da fadar shugaban kasar, shi ya jagoranci hambarar da gwamnatin Ali Bongo Ondimba, wanda iyalinsa suka mulki kasar tsawon shekara 55.
Ana sa ran rantsar da Janar Oligui a matsayin shugaban mulkin soji na riko a ranar Litinin.
Baya ga Gabon, an gudanar da juyin mulki a kasashe biyar kenan a cikin shekaru uku a Afirka wadanda suka hada da Mali da Guinea da Sudan da Burkina Faso da kuma Nijar.
Sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen duk sun ki amincewa da mika mulki cikin dan lokaci domin komawa bariki.