Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sallami wasu ministoci biyar tare da naɗa wasu sabbi guda bakwai a ranar Laraba.

Kazalika ya sauya wa ministoci 10 ma'aikatun da suke aiki, yayin da sabbin ministocin da aka naɗa kuma za su jira tabbatarwa daga Majalisar Dattijan Ƙasar.

Shugaban Ƙasar ya kori Ministar Mata Uju-Ken Ohanenye da Ministar Yawon Bude Ido Lola Ade-John da Ministan Ilimi Tahir Mamman da Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane Abdullahi Gwarzo da Ministar Ci Gaban Matasa Jamila Ibrahim.

Sai kuma ya ba da sunayen Bianca Odumegu-Ojukwu a matsayin Ministar Harkokin Waje, yayin da aka ba da sunan Nentawe Yilwatda a matsayin Ministar Jinƙai da Rage Talauci, lamarin da ya kawo ƙarshren mulkin Betta Edu wacce aka dakatar tun tuni.

A sanarwra da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar, an kuma ga sunan Maigari Dingyadi a matsayin Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Jumoke Oduwole Ministar Masana'antu da Idi Maiha Ministan sabuwar Ma'aikatar Bunƙasa Kiwo, da Yusuf Ata a matsayin Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane sai kuma Suwaiba Amhad a matsayin Ƙaramar Ministar Ilimi.

Sai kuma Shugaba Tinubu ya sanar da Shehu Dikko a matsayin sabon shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa.

Sannan Sunday Akin Dare ya zama sabon Mai BAi wa Shugaban Kasar Shawara na Musamman a kan Harkokin Sadarwar Jama'a wanda zai dinga aiki daga Ma'aikatar Watsa Labarai.

Shugaban ya gode wa ministocin da aka sallama din a yayin taron majalisar zartarwa da kuma yi musu fatan alheri a rayuwarsu ta gaba.

Sai kuma ya nemi sabbin ministoc da ma wadanda aka sauya wa ma'aikatu da su yi aiki tuƙuru don yi wa ƙasa hidima.

TRT Afrika