Shugaban Nijar Birgediya Janar Abdourahamane Tiani ya yi sabbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa inda ya naɗa sabbin gwamnoni a wasu jihohi da naɗa wani sabon jakada da kuma wani muƙami a cikin gida.
Shugaban ya naɗa Kanal-Manjo Bana Alhassane a matsayin gwamnan yankin Dosso inda ya maye gurbin Birgediya Janar Iro Oumarou wanda shi ne gwamnan yankin tun daga Agustan 2023.
Haka kuma shugaban ƙasar ya naɗa Kanal Massalatchi Mahaman Sani a matsayin sabon gwamnan Zinder inda ya maye gurbin Kanal Issoufou Labo wanda shi ne gwamnan yankin tun daga Yulin 2023.
Haka kuma an naɗa Abba Koulouma Djona a matsayin shugaban sashen Tassara, wanda muƙami ne da ke da alaƙa da aiwatar da tsare-tsare da kula da harkokin ƙananan hukumomi.
Daga cikin naɗe-naɗen da Shugaba Tiani ya yi har da naɗa Mohamed Anacko a matsayin jakada na musamman na Nijar a ƙasar Chadi.
An yi wannan naɗin ne domin ƙara yauƙaƙa dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu da ke makwabtaka da juna.
Haka kuma Shugaba Tiani ya naɗa Idrissa Djibo Maiga a matsayin Shugaban kamfanin sadarwa na Nijar, inda ya karɓi ragamar jagorancin ɓangaren daga Kanal-Manjo Ali Mahamadou wanda yake jagorantar kamfanin tun daga Nuwambar 2023.