Shugaban kamfanin BUA a Nijeriya Abdul Samad Rabiu ya yi watsi da mukamin da aka ba shi na mamba a kwamitin kudi na Jam’iyyar APC.
Abdul Samad din ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da kamfaninsa na BUA ya fitar a shafin X inda ya ce babu wanda ya tuntube shi kafin a ba shi wannan mukamin.
A ranar Juma’a ne Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da sunayen mambobin kwamitocinta wadanda suka hada da na gudanarwa da kudi da watsa labarai da harkokin gwamnati da sasanci.
A cikin kwamitin na kudi, baya ga Abdul Samad, akwai sauran hamshakan ‘yan kasuwa na Nijeriya da ke cikin kwamitin irin su Dahiru Mangal da A. A Rano da Alhaji Mohammed Indimi.
“Muna mika godiyar mu ga jam'iyyar APC bisa la'akari da shugabanmu kan irin wannan gagarumin aiki,” in ji sanarwar.
“Wannan karramawa ta nuna kokarinsa, da kuma na kamfanin BUA, wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasarmu Nijeriya. Sai dai yana da kyau a san da cewa shugabanmu, Abdul Samad Rabiu da kamfanin BUA ba su shiga siyasa tsawon shekaru.
“Wannan tsarin yana da nasaba da yanayin kasuwancinmu kuma ya yi daidai da yadda Rabiu ya mayar da hankali wajen inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar shirye-shiryen kungiyar BUA da kokarin taimakon jama'a ta hanyar shirin ASR Africa.
"Dangane da wannan, muna sanar da ‘yan jarida da abokan aikinmu da masu ruwa da tsaki, da sauran jama'a cewa Rabiu ya yanke shawarar kin amincewa da wannan mukamin,” in ji sanarwar.