Mamady Doumbouya ya yi wa Alpha Conde juyin mulki a Satumbar 2021. / Hoto: Reuters

Shugaban Guinea Mamadi Doumbouya ya yi wa kansa ƙarin girma zuwa muƙamin cikakken janar.

Doumbouya, mai shekaru 43, ya kwace mulki ne da karfin soji a watan Satumbar 2021 ta hanyar hamɓarar da shugaba Alpha Conde, wanda ya dora wa Doumbouya mai muƙamin kanal a wancan lokaci alhakin kula da wata runduna ta musamman domin bai wa shugaban ƙasa kariya.

Shugaban sojin ƙasar a watan Janairu ya ƙara wa kansa muƙami zuwa laftanar janar inda ya jaddada cewa sojojin ƙasar za su cika alƙawarin da suka ɗauka na miƙa mulki ga farar hula a ƙarshen shekara.

A wata doka da aka karanto yammacin Juma'a, Doumbouya, wanda magoya bayansa suka bukaci ya tsaya takarar shugaban kasa a lokacin da sojojin ƙasar ke son mika ragamar mulki ga farar hula -- an ba shi lambar yabo ta Grand Cross of the National Order of Colatier, wadda ita ce lambar yabo mafi girma a ƙasar.

An ba shi lambar yabo ne sakamakon yunƙurinsa na ƙara haɗa kan jama’ar ƙasar.

Ƙarin girman da Janar Doumbouya ya yi wa kansa na zuwa ne kwanaki bayan takwaransa na Mali Assimi Goita shi ma ya yi wa kansa ƙarin girma daga muƙamin kanal zuwa cikakken janar.

Doumbouya na daya daga cikin jami'an soji da dama da suka kwace mulki a yammacin Afirka tun daga shekarar 2020, tare da wasu shugabannin sojoji a Mali, Burkina Faso da Nijar.

AFP