Shugaba Felix Tshisekedi da shugaban da ya gada Joseph Kabila sun kasance abokan siyasa na kut da kut amma a zaɓen shekarar 2019 suka raba gari. Hoto / Reuters  

Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Felix Tshisekedi ya zargi tsohon shugaban kasar Joseph Kabila da goyon bayan ƙawancen kungiyoyin 'yan tawaye da Amurka ta amince da su a wata hira da wani gidan rediyo mai zaman kansa a ƙasar ya yi da shi a ranar Talata.

''Joseph Kabila ya ƙaurace wa zaben ƙasa kuma yana shirin ta da kayar baya saboda shi ne AFC,'' in ji Tshisekedi, yana mai cewa ƙawancen siyasa da sojoji na Alliance Fleuve Congo da aka ƙaddamar a watan Disamba da nufin hada kan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da jam'iyyun siyasa da kuma ƙungiyoyin farar hula don yakar gwamnatin Congo.

Bai dai bayar da wata hujja da za ta tabbatar da zargin nasa ba.

Zargin Tshisekedi ya biyo bayan sanarwar da Amurka ta yi na ƙaƙabawa AFC takunkumi a watan da ya gabata.

Kifar da gwamnati

Tshisekedi da Amurka da kuma kwararrun a Majalisar Dinkin Duniya, sun zargi maƙwabciyar ƙasar Rwanda da baiwa ƙungiyar M23 goyon bayan soji.

Rwanda dai ta musanta wannan zargi, sai dai a watan Fabraibu ta yarda da cewa ta jibge sojoji da na'urorin makamai masu linzami a gabashin Congo don kare tsaronta, tana mai nuni da tarin dakarun Congo da aka jibge a kusa da iyakarta.

A makon da ya gabata ne Congo da Rwanda suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ta soma aiki a ranar Lahadi bayan da Angola ta shiga tsakani.

Kisan ƙare-dangi

Yankin Gabashin Congo dai na fama da tashe-tashen hankula inda ƙungiyoyi sama da 120 ke fadan neman madafun iko da kasa da kuma albarkatun ma'adinai masu daraja a ƙasar, yayin da wasu ke kokarin kare al'ummominsu.

Kazalika, ana zargin wasu ƙungiyoyi da ke dauke da makamai da aikata kisan ƙare- dangi.

Rikicin ya fi ƙamari ne a gabashin lardin Kivu ta Arewa inda ba kisan gilla kadai ake yi ba har da cin zarafin mata ta hanyar lalata da su.

Fiye da mace ɗaya cikin mata 10 waɗanda suke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin sun bayar da rahoton yi musu fyade a tsakanin watan Nuwamba na 2023 zuwa Afrilu na 2024, in ji wani rahoto da kungiyar Doctors without Borders ko MSF ta fitar a ranar Talata.

“A cikin sansanoni uku da muke aiki, mun yi jinyar fiye da mutane 1,700 da suka tsira daga cin zarafinsu ta hanyar lalata a watan Afrilu, a kashi 70 cikin 100 na rahotannin da muka tattaro, masu ɗauke da makamai ne suke aikata wadannan aika-aika na ta'addanci," in ji Laura Garel, mai ba da shawara kan harkokin sadarwa a MSF.

AP