A ranar 29 ga watanb Mayu ne shugaban zai mika mulki ga Bola Tinubu. Hoto/Fadar Shugaban Nijeriya

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai tsawaita zamansa a Landan domin ganin likitan hakori.

Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmed ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce Shugaba Buhari, wanda ya je Landan domin halartar nadin Sarkin Ingila Charles III, zai kara mako guda a kasar ta Ingila.

Ya bayyana cewa ya dauki matakin ne saboda likitansa na hakori ya bukaci ya tsaya domin a sake duba lafiyarsa.

“Likitan ya bukaci ya sake ganin shugaban kasar daga yau zuwa kwanaki biyar masu zuwa sakamakon don ya cigaba da duba shi,” in ji sanarwar.

A baya dai, Shugaba Buhari, ya sha zuwa Landan domin a duba lafiyarsa.

Ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban na Nijeriya zai mika mulki ga zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu.

TRT Afrika