Matakin da gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta dauka na yin amfani da kudaden kananan hukumomi wurin gina wata gada a cikin birnin Kano ya jawo wa Gwamna Abba Kabir Yusuf suka.
Gwamnatin ta jihar Kano, a wata takarda da ofishin Babban Akanta na Jihar ya fitar, ta amince a kashe kusan Naira biliyan goma sha shida domin gina gadar kasa da ta sama a unguwar Dan-Agundi da ke cikin birnin Kano.
Za a yi hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da gwamnatocin kananan hukumomi wurin gina gadar inda jiha za ta bayar da kashi 30 yayin da kananan hukumomi za su bayar da kashi 70, in ji takardar.
"Don haka Majalisar Zartarwa ta jiha ta amince a fitar da naira biliyan shida da miliyan dari uku da tamanin da tara" a matsayin kudin kafin-alkalami ga dan kwangilar da zai yi wannan aiki, in ji gwamnatin.
Sai dai tuni wannan mataki ya soma fuskantar suka daga wadanda suke gani bai kamata a yi amfani da kudin kananan hukumomi wurin gudanar da irin wannan aiki a cikin birni ba bayan kuwa su ne suka fi cancanta wurin samun ayyukan ci-gaba.
A gefe guda, wasu suna ganin gina gada a wannan lokaci da talakawa ke bukatar ayyukan wajibi kamar samar da ruwan sha da gina asibitoci da makarantu da sauransu, ba shi ne ya zama abu mafi muhimmanci ba.
Fitaccen lauyan nan na jihar Kano, Abba Hikima, ya yi tsokaci a kan hakan inda ya ce "Don Allah a tsayar da wannan aikin. Irin wadannan abubuwan ne suke sa wa mutane suke dauka gaba daya ashe 'yan siyasa irinsu daya.
Yanzu saboda Allah ina adalci a nan? Kauyukan Kano suna cikin mawuyacin hali... amma a dauko kudinsu a saka a gada guda daya?"
A baya dai, jami'an gwamnati mai ci sun rika sukar gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje kan gina gadoji, shi ya sa ma a wannan karon wasu suke sukarsu bisa shirin gina gadar ta Dan-Agundi.
Malam Abdul Aziz Abdul Aziz, mai taimaka wa shugaban Nijeriya kan watsa labarai, ya ce "Lokacin da na ga sanarwar gina waɗannan gadoji na yi wa wasu abokaina guda biyu personal message (saboda gudun magana a bainar jama'a ƴan baka su maida abin siyasa).
"Abin da na rubuta musu shi ne idan har mun ta sukar Ganduje a kan kashe maƙudan kuɗaɗe don gina gadoji alhali akwai bukatu na gaggawa ban ga dalilin yin shiru a kan gadar Tal'udu da sauran da Abba yake shirin yi ba."
Ita ma Nanerh Hawwerh cewa ta yi "Maganar gaskiya, ni kaina ba na goyon bayan wannan aikin, akwai kauyuka da suke da bukata fiye da wannan aikin. Don Allah mahunkunta su duba wannan al'amari."
Sai dai a nasa bangaren, Aliyu Dahiru Aliyu, ya ce: "Harkar ci-gaban jiha haduwa ake a yi tare. Kudin revenue da ake samu a jihar nan fiye da rabinsa a local governments ba su fi biyar zuwa shida na birni ake tattara su ba. Amma a haka ake diba a yi wa na Doguwa da na Tsanyawa aiki."
Kawo yanzu gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba ta yi raddi kan wannan batu ba, sai dai wasu na ganin za ta iya sauya matsayinta idan aka yi la'akari da shawarwarin da aka ba ta a baya kan wasu matakai da ta dauka, wadanda ba su yi wa mutane dadi ba.