Faransa ta aika da sojoji 4,000 zuwa yankin Sahel a karkashin wani shiri da ta kira 'Farmakan Barkhane'. Hoto: AA

Daga Mazhun Idris

Bisa dukkan alamu tasirin da Faransa ke da shi na karfin soji da tattalin arziki a nahiyar Afirka ya kusa karewa.

Ana kallon juyin mulkin Nijar a matsayin kawo karshen munanan manufofin da Faransa ta rika aiwatarwa tun zamanin mulkin-mallaka a Yammacin Afirka, daga yankin Sahel zuwa gabar tekun Guinea.

Kyamar Faransa ta dade tana ginuwa a zukatan mazauna yankin Sahel, wadanda ta kwashe tsawon zamani tana yi wa mulkin-mallaka.

Kusan dukkan su suna yin korafi na fama da rashin tsaro da rashin tabbas na yanayin siyasa da kalubalen tattalin arziki da matsalolin sauyin yanayi.

"Mutane na kara wayewa da fahimtar cewa zaman Faransa a Afirka yana amfanar ta ne kawai," in ji Dr Garba Moussa, wani mai nazari kan tattalin arziki dan kasar Nijar da ke zaune a Paris.

A cewarsa mutanen kasashe irin su Nijar ba za su ci gaba da zura ido suna kallon abin da kasar take yi ba don kawai ta taba yi musu mulkin-mallaka.

Bayan juyin mulkin Mali sojojin Faransa sun bar kasa inda suka koma Nijar. Hoto: AP

A shekaru goma da suka gabata an fuskanci zanga-zangar adawa da Faransa a Afirka, dukkan zanga-zangar faru ne bayan wasu abubuwa da suka auku da suka hada da juyin mulki.

"A matsayi na na dan kasar Nijar, zan iya cewa ban ga wani abu da ya amfane mu a shekaru 60 da muka yi muna mu'amala da Faransa ba. Babu wani da ya sauya ya kara kyau," in ji Mounkaila Abdou Seni, sakataren kungiyar masu fada a ji a shafukan sada zumunta da ke Yamai babban birnin Nijar.

Adawa da Faransa, ba goyon bayan juyin mulki ba

Dadewar da Faransa ta yi tana juya gwamnatocin kasashen da ta yi wa mulkin- mallaka na janyo matsala.

Seini ya shaida wa TRT Afirka cewa "Yakin da aka yi a Libya ya haifar da yaduwar makamai a hannun 'yan ta'adda da ke addabar Yammacin Afirka."

Tun 2020 ne nuna kyama ga Faransa ya yi kamari a yankin Sahel. Hoto: AP

Bayan juyin mulkin da ya kifar da zababben Shugaba Mohamed Bazoum daga kan mulki, an ga mutane na kai hari a ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai.

Seini, daya daga cikin wadanda suka kafa 'Cibiyar Nijar', wata kungiya da ke Yamai, ya bayyana cewa rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki ne suka sanya jama'a harzuka.

Ya yi nuni da cewa "Shekaru 10 da suka gabata, hadin kan tsaro da Faransa bai rage wani abu na tabarbarewar tsaro ba."

"Ba dukkan mutanen da suka shiga zanga-zanga da aka yi bayan sojoji sun kifar da gwamnati ne ke goyon bayan juyin mulki ba.

Kawai dai wata dama ce suka samu ta tabbatar da ganin an bar su su kula da arzikin ma'adinan da Allah ya hore musu. Babban ra'ayin da ake da shi, shi ne na 'arzikinmu ya zama namu', kuma ya zama za mu iya rayuwa ba tare da taimakon kasashen waje ba," in ji Seini.

Yankin Sahel na fama da juyin mulki, inda masu nazari ke kiransa da "Cibiyar juyin mulki".

Wannan yanki ya hada da kasashe hudu da ke magana da Faransanci wadanda a yanzu haka suna karkashin mulkin soja - Mali, Burkina Faso, Chadi da Nijar.

Masu goyon bayan juyin mulki sun kai hari ofishin jakadancin Faransa a Yamai: Hoto AFP

Ta hanyoyi da dama, shugabanni masu ra'ayin juyin mulki ne ke ingiza bore ga Faransa a Afirka ta Yamma.

Matasa masu karfi a jiki, sojoji masu kuzari na saurin ganin sun samu dama ta mallakar nahiyarsu, tun daga bangaren kishin Afirka zuwa 'yancin juya akalar tattalin arziki.

Babban abun da ke ba su nasara shi ne yadda ake nuna kyama ga Faransa, da kuma babbar bukatar rabuwa da 'yan mulkin-mallaka. Ta wata hanyar, sun kwace matsayin zama kadangaren bakin tulu ga Faransa a Afirka.

Lamarin dai ya fara da kifar da gwamnatin farar hula a Mali a 2020, a Guunea a 2021 da Burkina Faso a watan Janairun wannan shekarar.

A lokacin da zababbiyar gwamnati a Nijar ta fadi a watan Yuli, sai wannan mummunan aiki na karya dimokuradiyya ya janyo kungiyar ECOWAS ta fara neman goyon bayan mambobinta da kasashen duniya don mayar da halastacciyar gwamnatin Nijar kujerarta.

Amma ta yaya ECOWAS za ta fuskanci kiran yanke hulda da Faransa?

A matsayinta na kungiya da aka kafa kan doron diflomasiyyar bangarori daban-daban, nasarar shugabancin kungiyar yankin za ta tabbata ne idan har ta biya bukatar 'yan kasashen na kawo karshen sansanonin sojin Faransa da kudadenta da ake kashewa a kasashen.

A lokacin da nuna kyama ga Faransa ke karu wa, ana ganin yadda ake goyon baya Rasha sosai a yankin Sahel. Hoto: AFP

"Yan kasar Nijar ba sa bukatar abubuwa da yawa," in ji Seini. "Duk mun san cewa Faransa na dogaro da Uranium dinmu don su samar da lantarki a kasarsu. Mutane na zargin Faransa da taimaka wa 'yan ta'adda da ke kai mana hare-hare don su ci gaba da satar arzikinmu, suna barin kasarmu cikin talauci."

Matakin karshe

Babban abun da mafi yawan 'yan kasashen da ke magana da harshen Faransanci suke bukata shi ne kawai a yanke hulda da Faransa, a dukkan abubuwan da take yi na tatsar kasashen ta hanyar dabbaka manufofinta na mulkin mallaka ta sabuwar hanya.

Wannan abu na tirsasa shugabannin ECOWAS su kula sosai da batun nuna adawa ga Faransa a dukkan yankin.

A jawabinsa a lokacin da ya tura tawaga zuwa Nijar, Shugaban ECOWA kuma Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kungiyar ta yanki ba ta songoyon baya ko kyamar wata kasar waje.

TRT Afrika