Shekara 63 da samun 'yancin Nijeriya: Abu shida da suka kamata ku sani kan jawabin Shugaba Tinubu

Shekara 63 da samun 'yancin Nijeriya: Abu shida da suka kamata ku sani kan jawabin Shugaba Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ce yana "sane da wahalhalun" da 'yan kasar suke ciki, yana mai cewa "idanuna suna gani kuma zuciyata tana kunci".
Shugaba Bola Tinubu ya ce gyara yana da matukar radadi amma shi ne kadai hanyar samun ci-gaban kasa. Hoto/BAT

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana daukar wasu matakai na takaitaccen lokaci da za su faranta ran ma'aikatan kasar, wadanda ke cikin miliyoyin 'yan kasar da ke fama da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin fetur.

A jawabin da ya gabatar wa 'yan kasar ranar Lahadi na bikin cikar Nijeriya shekara 63 da samun 'yancin kai, shugaban kasar ya jaddada cewa gwamnatinsa ta cire tallafin man ne domin ba ya amfanar galibin 'yan kasar, yana mai cewa zai yi amfani da kudin wurin inganta rayuwar jama'a.

Ya kara da cewa ba ya jin dadin halin da 'yan Nijeriya suke ciki na kunci da tsadar rayuwa, yana mai cewa yana sane da hakan.

Shugaba Tinubu ya yi jawabin ne kwanaki kadan kafin kungiyar kwadago ta kasar ta soma yajin aikin da ta sha alwashin yi sakamakon tsadar rayuwar da 'yan kasar ke ciki.

"Ba na farin cikin ganin al’ummar kasar nan na fama da wahalar da ya kamata a ce an sauke ta a shekarun da suka wuce. Zan so a ce babu wadannan wahalhalun a yanzu. Amma dole ne mu daure idan muna son samun makoma ta gari," in ji shugaban Nijeriya.

A cewasa: "Mun fara daukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaiton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunkasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya, da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata".

Ga wasu abu shida da suka kamata ku sani game da jawabin Shugaba Tinubu:

  • Bisa tattaunawarmu da ‘yan kwadago, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, muna gabatar da karin albashi na farko inda za mu kara mafi karancin albashin gwamnatin tarayya ba tare da kara hauhawar farashi ba. A tsawon watanni shida masu zuwa, kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu karin Naira Dubu Ashirin da Biyar kowanne wata a albashinsu.

  • Domin kawo ci-gaba a yankunan karkara, mun kafa asusun tallafi kan samar da kayayyakin more rayuwa domin jihohi su bunkasa bangarorin da ke da muhimmanci a yankunansu. Tuni jihohi suka karbi kudi domin ba da tallafin sassauta radadin hauhawar farashin abinci da sauran bukatun yau da gobe.

  • Bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage farashin sufuri na da matukar muhimmanci. Dangane da haka ne muka bude wani sabon babi a fannin sufuri ta hanyar samar da motocin haya masu amfani da iskar gas a fadin kasar nan. Wadannan motoci za su caji kudi kalilan kusa da yadda ake biya a yanzu ba.

  • Ba da jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa gas za su fara isowa kasar nan saboda mun dauki matakan takaita lokacin da aka saba dauka kafin shigo da su. Kuma za mu kafa wurin bayar da horo a fadin kasa domin koyarwa da ba da sababbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana’antu.

  • Domin bunkasa samar da aikin yi da kudin shiga ga mazauna birane, mun samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da suka nuna alamar makoma ta gari. Haka kuma mun kara zuba jari a kanana da matsakaitan kamfanoni.

  • Daga wannan watan, za a kara gidaje miliyan 15 kan wadanda ake bai wa tallafin kudi kai-tsaye domin rage musu radadi.

TRT Afrika