Shugaba Tinubu ya taya Musulmai murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah. Hoto: Presidency

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarcin Musulman ƙasar da su dinga bin koyarwar Annabi Muhammad SAW a zamantakewarsu ta yau da kullum.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan watsa labarai Ajuri Ngelale ya fitar, mai ɗauke da saƙonsa na taya Musulmai murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah.

Ranar Laraba 27 ga watan Satumba ne za ta kama ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal, watan da aka haifi Annabi Muhammad SAW, wadda kuma wani kaso na al’ummar Musulmai ke bikin tunawa da ranar a faɗin duniya.

“Ya kamata Musulmai su yi bakin ƙoƙarinsu wajen bin koyarwar Annabi Muhammad. Akwai manyan darussa na sadaukarwa da jajircewa da juriya da sauƙin kai da kuma sadaukarwa da dukkanmu za mu iya koya daga rayuwar Annabin,” in ji sanarwar.

Shugaban ya ce baya ga bikin murnar zagayowar ranar, ya kamata kuma a yi amfani da damar hakan wajen zurfafa tunani da tsananta addu’o’i.

Ya kuma yi kira ga shugabannin addini da su yi amfani da damar wajen yi wa ƙasar addu’a tare da jan hankalin mabiyansu wajen ɗaukar darussa daga rayuwar Annabi Muhammad wajen nuna sadaukarwarsu ga ƙasar.

“Nijeriya tana kan wata gaɓa mai muhimmanci sosai. A yayin da gwamnati ke ɗaukr dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaron ƙasar da farfaɗo da tattalin arziki, muna buƙatar cikakken goyon bayan ƴan ƙasa wajen nuna kishin ƙasarsu da haƙuri da kuma addu’o’i.

Tabbas za a ga hasken abun a nan gaba,” shugaban ƙasar ya tabbatar. Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci Musulman da suke bikin Maulidin da su yi amfani da damar wajen taimaka wa mabuƙata da masu rauni albarkacin wannan lokaci, tare da yi wa Nijeriya da shugabanninta addu’a a kowane mataki.

TRT Afrika