Rundunar ‘yan sandan Jihar Delta da ke kudu maso kudancin Nijeriya ta ce ta kama wasu mutum 100 da take zargin ‘yan luwadi ne suna gudanar da bikin auren jinsi a wani otel a jihar.
A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Talata, inda mai magana da yawun rundunar ke jawabin yadda aka kama su, ana iya hango mutanen a zaune a yayin da kakakin rundunar ke jawabi.
“Rundunar ‘yan sandan Jihar Delta ta kama fiye da mutum 100 da ake zargin ‘yan luwadi ne suna gudanar da auren jinsi a wani otel," in ji mai magana da yawun 'yan sandan.
Yadda aka gano mutanen
Da yake jawabi kan yadda ‘yan sanda suka gano mutanen a cikin bidiyon, kakakin rundunar Bright Edafe ya ce “a ranar 27 ga watan Agusta ne da misalin karfe daya na dare sai ‘yan sanda da ke sintiri suka kama wani mutum mai suna Chuks Chinye, wanda ya yi shigar mata.
“Da suka kama shi sai ya gaya wa ‘yan sanda cewa shi dan fim ne da ya je Delta daga Lagos don yin fim. Amma da aka ci gaba da yi masa tambayoyi, sai Chuks ya bayyana cewa shi dan wata kungiyar ‘yan luwadi ce kuma suna da biki ne a Otel din Zee Bolos,” in ji Mista Edafe.
Kakakin ‘yan sandan ya ce a washegari ne suka dirarwa otel din da misalin karfe 2 na dare inda suka kama mutum 200 da suke zargin su, mafi yawansu sun yi shigar mata.
“Abin takaicin ma shi ne yadda muka ga biyu daga cikinsu a matsayin ango da amarya, da kuma bidiyon yadda aka gudanar da auren.
Rundunar ‘yan sandan ta ce bayan tantance wadanda ake zargin ne aka samu damar ware mutum da yawansu har aka gabatar da su a bainar jama’a a ranar Talata.
Dokar hana auren jinsi a Nijeriya
A shekarar 2014 ne aka kaddamar da dokar hana auren jinsu a Nijeriya, kuma tun lokacin hukumomi sun sha kama wadanda ake zargi da aikata hakan.
Dokar ta sanya cewa duk wanda aka kama da laifin auren jinsi ko hannu a ciki to zai sha daurin shekara 14 a gidan yari.
Kakakin ‘yan sandan Jihar Delta ma ya nanata hakan a wannan kamen da suka yi, inda ya ce “hakan bala’i ne kuma bai kamata mu dinga kwaikwayon kasashen Yamma ba. A Nijeriya muke kuma doke mu bi al’adarmu. Dole mu bi doka. Abu ne da ke bayyane karara,” ya ce.