Jibge sojojin zai taimaka wajen baiwa manoma da dama damar shiga gonakinsu, kamar yadda daraktar ayyuka da yada labarai na tsaro. / Hoto: AFP

Hedkwatar tsaro Nijeriya ta tabbatar da tura dakarun sojinta a yankin arewacin ƙasar, musamman a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar ƙasar.

A cewar babban ofishin tsaron Nijeriya, an tura sojojin ne domin samar da isasshiyar kariya da tsaro ga manoma daga ‘yan fashi da ‘yan ta’adda da sauran miyagun masu aikata laifuka a yankin.

''Tura sojojin zai taimaka wajen bai wa manoma da dama damar shiga gonakinsu, kamar yadda daraktan hulda da jama'a na rundunar tsaro Manjo Janar Edward Buba ya bayyana wa TRT Afirka Hausa a ranar Alhamis.

''Yayin da aka shiga lokacin damina, a yanzu haka an tura sojoji zuwa wasu jihohin Arewa, musamman a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya domin samar da tsaro da kariya ga manoma,'' in ji shi.

"Tsarin ya bai wa manoma da dama damar shiga gonakinsu don yin noma ba tare da samun wata matsala ba har ya zuwa lokacin da za a yi girbi," in ji shi.

Kazalika a 'yan kwanakin baya-bayan ne, babban Sifeto ‘yan sanda, Kayode Egbetokunya bayyana cewa an tura jami'an ‘yan sanda zuwa gonaki domin bai wa manowa ƙwarin gwiwa yin noma.

''Mun fara aikin sintiri a ganoki a yankunan jihohin Arewa maso Gabas don bai wa manoma ƙwarin gwiwar komawa gonakinsu, Shugaban ƙasa ya damu matuƙa kan wannan lamari, kuma muna kan iya koƙarinmu wajen tabbatar da hakan,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa yanayin tsaro a Nijeriya yana da sarƙaƙiya.

Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da ayyukan ‘yan fashi da ‘yan ta’adda da ke ɗaɗa janyo barna da koma baya a yankunan a cikin watanni shida da suka wuce.

Rahotanni da dama daga Nijeriya sun bayyana cewa an kashe daruruwan manoma tare da yin garkuwa da wasu a yankin a watanni huɗun farko na shekarar 2024.

Kazalika wani rahoto da shafin tattara bayanai na SBM Intelligence ya fitar, ya bayyana cewa manoma a Arewa sun biya kimanin Naira miliyan 139 a matsayin harajin noma ga ‘yan fashi bayana sun nemi a biyasu a kalla Naira miliyan 224 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023.

Lamarin da ya taimaka wajen hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya.

Hauhawar farashin abinci a Nijeriya ya karu zuwa kashi 40.87 bisa ga rahoton hukumar kiɗiɗɗiga ta kasa a watan Yuni.

TRT Afrika