Rundunar tsaron Nijeriya ta tabbatar da cewa jami'anta 36 ne suka mutu a Jihar Neja da ke yankin arewa ta tsakiyar kasar, sakamakon kwanton bauna da aka yi musu da kuma hatsarin jirgin soji.
Kakakin rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da aka yi a Abuja a ranar Alhamis.
Da yake yin bayani dalla-dalla kan yadda lamarin ya kasance, Manjo Janar Buba ya ce "An yi wa dakarunmu kwanton bauna a yankin karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja. Lamarin ya jawo musayar wutar da ya yi sanadin mutuwar jami'ai uku da sojoji 22 sannan soja bakwai kuma suka jikkata.
"A sakamakon hakan ne muka kaddamar da aikin jinkai don kwashe mamatan da wadanda suka ji rauni a wani jirgin rundunar sojin sama.
”A kan hanyar jirgin ta zuwa Kaduna ne sai ya yi hatsari. A cikin jirgin akwai gawarwakin mutum 14 na wadanda suka mutu a kwanton baunar farko, da bakwai din da suka ji raunuka, da matukan jirgin biyu da kuma ma'aikatan jirgin biyu," kamar yadda kakakin rundunar ya ce.
Kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa da aka tambaye shi karin bayani kan hatsarin helikwaftan, sai Manjo Janar Buba ya ce ana ci gaba da bincike don gano abin da ya jawo tare da jan hankalin 'yan kasa da su guji yarda da farfagandar da 'yan ta'adda ke yadawa tare da zama masu kishin kasa.
Masu tayar da kayar baya ne suka yi wa dakarun kwanton bauna a yankin Zungeru ranar Lahadi da mareceninda dakarun suka hadu da ajalinsu.
Shi kuma jirgin yakin rundunar sojin saman Nijeriya wanda ya je aikin ceton ya yi hatsari a ranar Litinin a yankin karamar hukumar Shiroro.