Sojoji 17 aka yi wa kisa gilla a jihar Delta da ke kudancin Nijeriya. Hoto: Rundunar sojin Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta fitar da jerin hotunan jami'anta da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta da ke kudancin Nijeriya a makon jiya.

Ta wallafa hotunan nasu ne a shafinta na X a yau Litinin da maraice, inda ta sake bayyana jimamin rashin da ta yi, wanda take zargin wasu ɓata-gari da aikata shi.

Sanarwar rundunar na zuwa ne a daidai lokacin da take zargin al'ummar ƙauyen Okuama na Jihar Delta da hannu a kitsa lamarin, tare da yaɗa farfaganda don "rufe aika-aikar da suka yi".

Wannan lamari ya faru ne a a ranar Alhamis, lokacin da sojojin suka kai ɗauki a wani rikicin ƙabilanci da ke faruwa tsakanin al'ummomi biyu na yankin.

Gwamnatin Nijeriya da ma al'ummar ƙasar sun yi Allah wadai da "wannan ta'addanci", inda Shugaba Bola Tinubu ya bai wa rundunar tsaron ƙasar "cikakken iko" na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan sojojin 17.

Yaɗa farfaganda

A sanarwar da ta fitar tun da fari a ranar Litinin da rana, rundunar sojin Nijeriya ta ce duk da mummunan kisan gillar da aka yi wa dakarunta a yankin, amma "abin takaicin shi ne yadda al'ummar wajen take amfani da kafafen watsa labarai wajen yaɗa farfagandar neman kare kansu, maimakon su taimaka wajen gano waɗanda suka aikata ɓarnar."

"Wannan kuma wata alama ce da ke nuna cewa al'ummar yankin ce ta kitsa wannan hari na kisan da aka yi wa sojojin," in ji rundunar.

Al'ummar yankin sun yaɗa labarin cewa sun ga mutane sanye da kakin soji suna ƙona gidaje a yankin, kwanaki kaɗan bayan da "matasa suka kashe dakarun" waɗanda aka aika su don magance wani rikici da ake yi a kan wajen zama.

Amma rundunar ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su yi watsi da labaran da al'ummar yankin ke yaɗawa, tana mai cewa suna yin hakan ne don neman kare kansu.

"Wadannan sojoji ne da suka jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ƴan kasa da ma waɗanda ba ƴan kasa ba a yankin Neja-Delta, waɗanda wasu gungun matasa ɗauke da makamai na al’ummar Okuama suka yi wa kisan gilla ta hanyar rashin imani, sannan suka wulaƙanta gawawwakinsu inda har suka fasa ƙirajensu suka ciro zuciyoyinsu, a matsayinsu na mutanen da aka tura dakarun don su ba su kariya," rundunar ta koka.

Sojojin waɗanda suka haɗa da kwamanda ɗaya da masu muƙamin manjo guda biyu da kyaftin ɗaya da kuma ƙananan sojoji 13 sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki wurin wani rikicin ƙabilanci a ƙauyen Okuama.

Sunayen dakarun da aka kashe

  • Laftanal Kanal AH Ali
  • Manjo SD Shafa
  • Manjo DE Obi
  • Kyaftin U Zakari
  • Sajan Yahaya Saidu
  • Cpl Yahaya Danbaba
  • Cpl Kabiru Bashir
  • LCpl Bulus Haruna
  • LCpl Sole Opeyemi
  • LCpl Bello Anas
  • LCpl Hamman Peter
  • LCpl Ibrahim Abdullahi
  • Pte Alhaji Isah
  • Pte Clement Francis
  • Pte Ibrahim Adamu
  • Pte Abubakar Ali
  • Pte Ibrahim adamu
  • Pte Adamu Ibrahim

TRT Afrika