Faransa ta kara yawan dakarunta a Nijar a 2021 bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun kore ta daga can. / Hoto: AP  

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sojoji 400 na Faransa da ke garin Ouallam na kudu maso yammacin kasar za su kasance rukunin farko da za su fice daga kasar a wannan makon.

Wata sanarwa da aka karanta a gidan rediyo na kasar ranar Alhamis ta ce nan da karshen shekarar nan za a rufe sansanin sojin Faransa da ke Yamai.

Faransa ta ce za ta kwashe dakarunta daga Nijar a karshen makon nan bayan a watan jiya shugaban kasar Emmanuel Macron ya ce sojojin Nijar ba su isa su bude masa ido ba.

Sai dai daga bisani Mr Macron ya yi amai ya lashe inda ya ce zai janye dakarunsa da kuma jakadansa daga Nijar.

Matakin da Faransa ta dauka na janye dakarunta 1,500 daga Nijar, inda suka kwashe shekara da shekaru suna yaki da mayakan da ke alaka da Al Qaeda da ISIS a yankin Sahel, wani babban abin kunya ne a gare ta.

Hedikwatar sojin Faransa ta ce sojojinta suna bukatar tsaro, ciki har da kariya ta sama, kafin su fita daga sansaninsu don ficewa daga Yamai, babban birnin Nijar.

Sojojin Nijar sun ce za su tabbatar da ganin dakarun Faransa sun fita daga kasar cikin tsanaki. Sun yi kira ga 'yan kasar su sanya ido a yayin da sojojin Faransa ke shirin fita daga kasar.

Faransa ta kara yawan dakarunta a Nijar bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun kore ta daga can, inda ta aika karin jiragen helikwafta da jirage marasa matuka da jiragen yaki.

TRT Afrika da abokan hulda