Rushewar wani dogon bene da ake ginawa a birnin George na Afirka ta Kudu ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum hudu yayin da fiye da hamsin kuma suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai, a cewar hukumomi ranar Talata.
Hukumomin jihar sun ce kawo yanzu, an tono mutum 24 daga cikin ɓaraguzai, hudu daga cikinsu sun mutu, har yanzu kuma na neman mutum 51.
Ma’aikata 75 ne a wajen lokacin da ginin ya rushe da yammacin Litinin.“
Tawaga uku ta masu aikin ceto a yanzu haka na aiki a ɓangarori daban-daban na wajen da ake ginin da ya rushe,” a cewar sanarwar.
Mai magana yawun wata kungiyar agaji, Gift the Givers da ke taimakawa wajen ceto mutanen da ginin ya rufta da su Mario Ferreira, ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa masu aikin ceton suna “magana da mutanen da ke karkashin ɓaraguzai.”
Ginin mai hawa biyar da kuma wajen ajiye motoci na ƙarƙashin kasa, ya rufta ne da yammacin Litinin, sai dai har yanzu ba a san dalilin rushewarsa ba.
"Akwai mutanen da aka kwashe su wadanda sun ji mugun rauni," a cewar Ferreira. Wani ma’aikacin agaji da wani kare mai gano inda mutane suke, na daga cikin muaten da ke ƙarƙarshin ɓaraguzan a George.