Kungiyar kwallon kafa ta Roma ta karbi aron dan kasar Belgium Romelu Lukaku daga Chelsea tsawon kakar wasa daya zuwa ranar 30 ga watan Yuni 2024.
Ba a fadi kudin da kungiyar ta sayi dan wasan ba amma kafafen watsa labaran Italiya sun ce darajarsa ta kai $8.70m, ciki har da tsarabe-tsarabe.
"Muna yi wa Romelu Lukaku barka da zuwa. Kungiyar tana farin cikin tabbatar da cewa ta dauki fitaccen dan wasan Belgium," a cewar sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Alhamis.
Lukaku ya zura kwallo 280 a wasa 589 da ya buga. Ya lashe gasar Zakarun Kwallon Kafar Belgium a kungiyar Anderlecht, da FA Cup da Gasar Kofin Duniya ta Kungiyoyi a Chelsea, da kuma Scudetto, Italian Cup, da Italian Super Cup a Milan.
"Tarbar da na samu a wannan kungiya da kuma magoya bayanta ta sanya ni farin ciki. A matsayina na dan wasa na kungiyar da ke hamayya, na ji dadin shigowa filin wasan Stadio Olimpico, da kuma ganawa da 'yan Romania," in ji Lukaku.
"Kwanakin baya na samu damar tattaunawa da masu kungiyar nan, kuma na ji dadin abubuwan da suke son cimma. Yanzu, dole mu yi aiki, mu yi kaskan da kai sannan mu habaka wasan kwallon kafa."
Tiago Pinto, janar manajan Roma, ya ce zuwan Lakaku kungiyar ya sa "mun samu kwararre wanda zai sa mu yi nasara."
Dan wasan mai shekara 30 zai sanya riga mai lamba 90.