Rikici a yankin Darfur na kasar Sudan da aka dade ana fama da shi ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 14 a cikin kwanaki ukun da suka gabata, a cewar wasu masu fafutuka biyu.
Adam Haroun, wani mai fafutuka a yankin, ya bayyana cewa rikici ya barke a ranar Lahadin da ta gabata a lardin yammacin Darfur bayan da wasu ‘yan bindiga kan babura suka harbe wani dan kasuwa a kauyen Fur Baranga.
Kisan ya haifar da hare-haren ramuwar gayya tsakanin kungiyoyin kabilun Larabawa da na Afirka har da kuma kwasar ganima, in ji Adam Regal, mai magana da yawun wata kungiyar da ke taimaka wa sansanonin ‘yan gudun hijira a Darfur.
An ci gaba da rikicin har zuwa ranar Talata kuma akwai yiwuwar adadin wadanda suka muta ya karu, in ji Haroun.
A ranar litinin, gwamnan yankin yammacin Darfur ya ayyana dokar ta-baci na tsawon makonni biyu tare da kafa dokar hana fita ta dare a fadin jihar.
Manazarta na ganin an dada samun tashe- tashen hankula a 'yan watannin baya-bayan nan tsakanin kungiyoyin kabilu daban-daban a yankuna masu nisa na Sudan, sakamakon karfin iko da kuma tashe-tashen hankula da rikicin siyasa ya haifar.
Tashe- tashen hankula
A karshen watan Maris, an kashe akalla mutane biyar a wani fada da ta barke a yammacin Darfur.
A watan Oktoban da ya gabata, sama da mutane 170 ne aka kashe a wani rikici a lardin Blue Nile da ke wani kauye a yankin kudu maso gabashin kasar.
Sudan ta fada cikin rudani tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da ya hambarar da gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen Yamma a watan Oktoban 2021 da ya yi sanadiyar kawo karshen mulkin dimokradiyya.
Karkashin tsanani matsin lamba na kasa da kasa, sojojin da ke rike da mulki a Sudan da dakarun dimokaradiyya daban-daban suka rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar ta farko a watan Disamba, inda suka yi alkawarin maido da sauye-sauyen da aka yi wa tsarin demokradiyyar kasar
Bayan shafe tsawon watanni ana takun saka, an yi ta tattaunawar tsakanin jam'iyyu da Majalisar Dinkin Duniya da sauran masu ruwa da tsaki na kasa da kasa amma bangarorin siyasa a Sudan har yanzu sun ki amincewa a samar da yarjejeniyar karshe.
Mayakan Sudan dai na ci gaba da nuna adawa da yarjejeniyar.
Rikicin Darfur ya fara barkewa ne a shekarar 2003 lokacin da 'yan tawaye wadanda akasarinsu daga yankin ‘yan kabilar tsakiya da ‘yan yankin kudu da hamadar sahara suka kaddamar da tawaye, suna korafin zaluncin da gwamnati da ke Khartoum.
Gwamnatin wancan lokacin karkashin jagorancin Bashir, ta mayar da martani ne da wani harin bama-bamai ta sama da kuma luguden wuta da mayakan Janjaweed suka yi.
Tsawon shekaru nan, an kashe mutane kusan dubu 300 kuma an raba mutane miliyan 2.7 daga matsuguninsu a Darfur.