Yawan mutanen da suka rasa matsugunansu a Afirka ya ƙaru zuwa adadin da bai taɓa kai wa ba a wannan shekara, sakamakon rikice-rikice da "zalunci".
A wannan lokaci an yi rijistar mutane da suka kai miliyan 45 na waɗanda suka tagayyara (IDPs) da masu neman mafaka a Afirka.
Wannan na nufin nahiyar a yanzu tana ɗauke da kusan rabin yawan adadin na duniya, a cewar rahoton cibiyar Africa Center for Strategic Studies.
Yawancin mutanen an tilasta musu ƙauracewa gidajensu sakamakon rikice-rikice kamar na Sudan da gabashin Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo, wadda ba ta da alamar ƙarewa.
Ninkin adadi
Rahoton ya gano cewa adadin waɗanda suka tagayyara a nahiyar ya ƙaru a karo na shekara ta 13 a jere, kuma yana dab da ninkawa sau uku da aka gani a shekaru bakwai da suka gabata.
A Sudan an samu mutane miliyan 12.6 da suka tagayyara zuwa tsakiyar shekara, kuma shi ne ɗaya cikin tara na ƙasashen Afirka da ke fama da ƙaruwar masu tagayyara.
"Sudan tana da mafi yawan mutanen da suka tagayyara a duniya, kuma ta samar da kaso na biyu mafi yawa na adadin jimillar mutanen da suka tagayyara a duniya, wanda a yanzu ya kai sama da mutane 12.6 million, idan an kwatanta da adadin na Syria, wanda ya kai kusan miliyan 13.8," cewar rahoton.
Wani yanayi mafi muni na sauran ƙasashen Afirka shi ne na Congo (DRC), da Somalia, da Nijeriya, da Habasha, da Sudan ta Kudu, da Burkina Faso, da Kamaru, da Jumhuriyar Tsakiyar Afirka (CAR).