Daga Kudra Maliro
Saura kwanaki kadan a gudanar da zabe a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, inda ake sa ran gudanar da zaben kasar a ranar 20 ga watan Disamba.
A daidai lokacin da ‘yan takara ke ci gaba da zuwa yankuna domin neman goyon bayan masu zabe, abu daya ne ya zama tabbas – wato mata kadan ne a zaben kasar idan aka kwatanta da maza.
TRT Afrika ta tattauna da mata da dama – masu zabe da ‘yan takara – kan yadda suke ji dangane da wannan zaben da kuma abin da ya fi damunsu. Amsoshin da suke bayarwa sun fi karkata wurare biyu: wato batun tsaro da kuma ci gaba.
Delice Kawaya, wadda me sanin makamar aikin gwamnati ce a gabashin birnin Beni, ta bayyana cewa za ta dangwalawa shugaban kasa mai ci a yanzu Felix Tshisekedi domin ya ci gaba da gudanar da ayyuka.
‘Shugabanni na gari’
Kamar yadda ‘yar kasar mai shekara 23 ta bayyana, shugaban kasan ya samar da tsare-tsare wadanda za su taimaka wurin yaki da kungiyoyi masu rike da makamai a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
“Akwai lokutan da mutane da ke zaune a wajen birnin Goma aka tilasta musu barin gidajensu domin samun wuri mafi aminci.
“Mata ne suka fi shan wahala, sakamakon wasu daga cikinsu ana cin zarafinsu ta hanyar lalata domin ba su abinci da wurin zama,” kamar yadda Kawaya ta bayyana inda ta ce yanayin tsaro a Goma ya gyaru duk da cewa akwai sauran jan aiki a gaba.
Natalie Maliva wadda ta kammala karatun likita kuma ‘yar gwagwarmaya ta bayyana cewa “shugabanni na gari ne kadai za su iya sauya Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.”
‘Kokarin yin komai’
“Idan muka zabi mutanen da ba su dace ba, za mu iya samun ci baya ne kawai a matsayinmu na kasa,” kamar yadda ta bayyana.
“A Kongo, za mu iya yin komai (wa kanmu). Za mu iya gina kamfanoni da tituna da asibitoci da kanmu. Sai dai hakan zai iya yiwuwa ne kadai idan muna da kasa mai aminci,” in ji Maliva.
A yayin da Maliva da Kawaya na neman yadda za su jefa kuri’arsu a ranar 20 ga watan Disamba, Alice wadda ta kammala karatun aikin gona ta bayyana cewa ba za ta yi zabe ba saboda “babu abin da zai sauya.”
Mata da suka tsaya takara wadanda ba su da yawa idan aka kwatanta da maza, sun fuskanci matsaloli domin daukar dawainiyar yakin neman zabe – tun daga kan karancin kudi da kuma wariyar jinsi.
Gaza fita yakin neman zabe
Neema Kamabu, wadda ‘yar takara ce ta dan majalisa, har zuwa yanzu ba ta fita zabe yakin neman zabe ba, ga shi kuma saura kwana hudu zabe.
Zuwa yanzu ta buga fastoci kadan ne kawai sakamakon karancin kudi. Kamabu ta sadakar kan cewa ta fadi zabe.
“A halin yanzu zan mayar da hankali kan zaben 2028 da ke tafe. Babu wata hanya da za ta bulle mani a bana.”
Ta bayyana cewa jam’iyyarta ta mata alkwarin kudin yakin neman zabe sai dai ba su cika alkawarin ba.