Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kira kan a samar da mafita wajen warware rikicin siyasar Nijar cikin lumana.
Putin ya bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita, a cewar sanarwar da Fadar Kremlin ta fitar a ranar Talata.
"An jaddada muhimmancin warware al'amura da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar musamman kan siyasa da diflomasiyya ta hanyar lumana," a cewar sanarwar.
Putin ya yi ta ganawa da shugabannin kasashen Yammacin Afirka da ke mara wa sojojin da suka hambarar da gwamnatin farar hula ta shugaban kasar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.
Ana sa ran manyan hafsoshin sojin kungiyar ECOWAS za su yi wata ganawa a ranar Alhamis da Juma'a don tattauna hanyoyin shiga soji Nijar, a cewar sanarwar da wasu majiyoyin suka fitar a ranar Talata.
A baya dai an shirya gudanar da taron ne a ranar Asabar, amma kuma aka dage shi -sai da aka gudanar da taron shugabannin ECOWAS a makon da ya gabata, inda aka amince da ranar tare da neman a ''aika da rundunar soji da za ta yi aikin maido da tsarin mulki a Nijar''.