Hambararren tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir / Hoto: AA

An dauke hambararren Shugaban Sudan Omar al-Bashir daga gidan yarin Kober zuwa asibitin soji da ke Khartoum babban birnin kasar, kafin a soma gwabza kazamin fadan da ya barke a kasar a ranar 15 ga watan Afrilu, kamar yadda wasu majiyoyi biyu na asibitin suka bayyana.

An dasa ayar tambaya kan inda Bashir yake bayan da wani tsohon minista a zamanin mulkinsa, Ali Haroun a ranar Talata ya ce tsohon shugaban ya bar gidan yarin tare da wasu tsofaffin jami’an gwamnati.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC na neman Bashir da Haroun, bisa tuhumar ta'addancin da ake zarginsu da aikatawa a yankin Darfur.

Fada ya sake barkewa a Sudan da yammacin ranar Talata duk da sanarwar tsagaita wuta da bangarorin da ke fada da juna suka bayar, yayin da mutane da dama ke kokarin tserewa daga Khartoum cikin yanayi na tashin hanakali.

Dakarun sojin Sudan ta SAF da dakarun RSF sun amince da tsagaita bude wuta na sa'o'i 72 da ya kamata a fara ranar Talata bayan shawarwari da Amurka da Saudiyya suka bayar.

Sai dai an yi jin karar ''harbe-harbe da fashe-fashe a tsakiyar dare a Omdurman, daya daga cikin biranen kusa da Khartoum da ke daf da kogin Nilu inda soji ke amfani da jirage marasa matuka wajen kai hari kan wuraren da dakarun RSF suke,'' in ji wani dan jaridar Reuters.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Sudan Volker Perthes ya fada wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata cewa " ya zuwa yanzu da alama an soma tsagaita bude wuta a wasu sassan kasar."

Sai dai ya ce har yanzu babu daya daga cikin bangarorin biyu da ya nuna shirin a yi wata "yarjejeniyar tattaunawa ta gaske na neman sulhu, yana mai nuni da cewa ko wane su na ganin akwai yiwuwar samun nasara kan dayansu.

"Wannan rashin dabara ce," in ji Perthes, ya kara da cewa filin jirgin saman Khartoum yana aiki amma hanyoyin duk sun lalace.

‘Yan Turkiyya na farko da aka kwaso daga Sudan sun isa Santambul a ranar Laraba kuma Saudiyya ta ce ta kwashe 'yan kasarta su 13 da wasu mutane 1,674, ba tare da ganin wata alama ta cewa bangarorin na shirin zama a teburin yin sulhu ba.

Kamfanin jirgin saman Turkish Airlines ya kwaso Turkawan ne daga Addis Ababa, babban birnin Habasha bayan sun isa can da motoci.

Ana sa ran nan gaba a ranar Laraban wasu karin jiragen za su kwaso sauran ‘yan Turkiyya da suka tsallaka zuwa Habasha daga Sudan.

TRT Afrika