Hukumar NYSC mai kula da yi wa Nijeriya hidima ta ce matan aure za su iya sauya jiharsu ta yi wa kasa hidima ba tare da sun yi wata doguwar tafiya ba.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce: “Duk masu yi wa kasa hidima da aka tura jihohin da ba nan mazajensu ke da zama ba, su garzaya sansanin horar da masu yi wa kasa hidima da ke kusa da su don a sauya musu jihar da za su yi wa kasa hidima.”
Hukumar ta sharwaci matan cewa su je sansanin horar da masu yi wa kasa hidimar da takardun shaidar aurensu da sauran takardu da za su tabbatar da cewar sun yi auren don a sauya musu jihar yi wa kasa hidima.
Kafin hukumar ta fitar da wannan sanarwar, ba a sauya wuri ko jihar yi wa kasa hidima sai an je sansanin horar da masu yi wa kasa hidima a jihar da aka tura mutum.
Alal misali a baya, wadda aka tura jihar Ogun yi wa kasa hidima daga jihar Kano sai ta je jihar Ogun din kafin a sauya mata jihar yi wa kasa hidima.
A kowace shekara, dubban matasa maza da mata ‘yan Nijeriya ne suke kwashe shekara daya suna yi wa kasar hidima bayan sun kammala karatun digiri ko HND kuma ba su wuce shekara 30 ba.
Dokar Nijeriya ba ta yarda wanda ya kammala karatun digiri ko HND a lokacin da bai kai shekara 30 ya yi aiki ba tare da ya yi wa kasar hidimar shekara daya ba.