Mai Bai Wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro a Nuhu Ribadu, ya zargi wasu bara-gurbi a jami'an ‘yan sanda da soji da sayar da makamai ga ‘yan bindiga.
Ribadu ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Alhamis a yayin da ake lalata makamai ƙarƙashin jagorancin Cibiyar Yaƙi da Mallakar Ƙananan Makamai ta Nijeriya.
Mai Bayar da Shawara Kan Sha’anin Tsaro ya ce jami’an tsaron da ke irin wannan aika-aika "mutane ne mafiya muni", yana mai ƙarawa da cewa dole ne a ɗauki matakan hukunta irin waɗannan mutanen.
Ya ce “Ya zama wajibi mu lalubo hanyar dakatar da wannan ta’annati idan muna son farfaɗo da ƙasarmu da kuma yin rayuwa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
“Ɗan'adam mafi muni shi ne ɗan sanda ko soja da zai saci makamai daga wajen aikinsa ya sayar wa ɓata-gari su zo suna kashe abokan aikinsu,” in ji Ribadu.
Ribadu ya kuma tsine wa ma’aikatan tsaro da ke da hannu wajen kai makamai ga ‘yan ta’adda da sauran ɓata-gari, inda ya ce yawancin makaman da ake aikata laifi da su a Nijeriya mallakin gwamnati ne.
Boko Haram da sauran ƙungiyoyin da ke tayar da ƙayar baya suna kai hare-hare tun tsawon shekaru 15 a arewa maso-gabashin Nijeriya tare da kashe fiye da mutane 40,000.
A watan Afrilu ‘yan ta’addar Boko Haram sun kashe sojoji biyu tare da wasu ‘yan sa-kai da ke gadin ƙauyen Allawa, daga nan aka janye dakaru daga ƙauyen wanda hakan ya sanya jama’ar yankin guduwa.
Tsawon shekaru yankunan tsakiya da arewa maso-yammacin Nijeriya na fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman fansa.
Ana zargin wasu jami'an tsaro da haɗa baki da waɗannan 'yan ta’adda ta hanyar sayar musu makamai don kai hari a suna kashe mutane tare da ƙona garuruwansu.