NLDEA ta kama dalibin da ya boye kwaya a cikin ‘crayfish’

NLDEA ta kama dalibin da ya boye kwaya a cikin ‘crayfish’

NDLEA ta ce ta kama dalibin a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Turai domin karatu.
NDLEA ta ce kilo 7.2 na kwayar methamphetamine ne kunshe a cikin kifin. Hoto/NDLEA

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta kama wani dalibi bisa zarginsa da yunkurin fitar da kwaya zuwa Turai.

Hukumar ta kama Benjamin Nnamani Daberechi, mai shekara 19, da kilo 7.2 na kwayar methamphetamine wadda aka boye a cikin ‘crayfish’.

A sanarwar da NDLEA ta fitar a ranar Lahadi, ta ce Benjamin dalibi ne da ke shirin zuwa kasar Cyprus karatun digiri.

“An kama matashin da ake zargi a ranar Laraba 12 ga watan Yuli, a lokacin da ake duba fasinjojin jirgin Turkiyya mai lamba 0624.

“Bayan jami’ai sun masa tambayoyi, Daberechi ya yi ikirarin shi dalibi ne wanda ke hanyarsa ta zuwa Cyprus karatu, sai dai bayan bude jakarsa sai aka gano kilo 7.2 na wani farin abu da aka kunshe a cikin buhun ‘crayfish’”.

Hukumar ta bayyana cewa bayan an gudanar da gwaji sai aka gano cewa kwayar Methamphetamine ce.

A yakin da hukumar ta NDLEA ke yi da fataucin miyagun kwayoyi, hukumar ta ce jam’anta sun kama kilo 116.5 na tabar wiwi nau’in Colorado a tashar ruwa ta Tincan.

Ta bayyana cewa an boye wiwin ne a cikin buhuna inda aka boye su a kasan gwanjon kayayyakin mota da ke cikin kwantena.

Hukumar ta ce ta yi kamun ne da taimakon hukumar kwastam da DSS da sauran masu ruwa da tsaki. Safarar miyagun kwayoyi babbar matsala ce a Nijeriya duk da irin samame da kuma kamen da hukumar ta NDLEA take yi.

Domin ko a makon da ya gabata sai da hukumar ta kama jami’an coci biyu kan zargin safarar miyagun kwayoyi a birnin Warri na Jihar Delta.

TRT Afrika