NLC ta ce dole gwamnatin Nijeriya da CBN su saki isassun takardun kudi domin 'yan kasar su daina fuskantar wahala / Hoto: Reuters

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga a fadin kasar sakamakon karancin takardun kudi a hannun jama'a.

Kungiyar ta bayyana haka ne ranar Talata da maraice a wata sanarwa da shugabanta na kasa Joe Ajaero ya fitar.

NLC ta bayyana takaici game da yadda bankunan kasar suka kasa wadata na'urorin cire takardun kudi na ATM da tsabar kudi, sannan ta soki Babban Bankin kasar da yin biris kan mawuyacin halin da 'yan Nijeriya suke ciki na karancin takardun kudi.

Ajaero ya ce rashin isassun takardun kudin ya jefa tattalin arzikin Nijeriya da 'yan kasar cikin mawuyacin hali musamman a yayin da ake dab da soma shagulgunan Kirsimeti da karshen shekara.

"Har yanzu 'yan Nijeriya ba su manta da matsanancin halin da aka jefa su a ciki sakamakon karancin takardun kudi a farkon shekarar nan ba, matakin da shugabannin da suka gabata mara kan gado don sake fasalin kudi,"in ji NLC.

"Wannan karo, babu wani dalili da Babban Bankin Nijeriya (CBN) da kuma gwamnati suka bayar game da dalilin da aka jefa 'yan Nijeriya cikin karin mawuyacin hali a 2023.

Duk da yake mun ji an ce akwai karin jabun takardun kudi a hannun jama'a da kuma boye Naira. Ba za a amince da wadannan dalilai ba domin ba mu ga wasu hujjoji da za su sa dan Nijeriya ya boye Naira ba. Kuma ai ba gama-garin 'yan Nijeriya ne suke biye kudi a gidajensu ba," a cewar NLC.

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya ta ce idan dai CBN na nufin cewa mutanen da suka mallaki kudi ta haramtacciyar hanya ce suke boye kudi domin gudun kada a gano su, hakan kalubale ne ga hukumomin gwamnati da ke yaki da cin hanci.

NLC ta ce abin takaici shi ne yadda 'yan Nijeriya suke bata lokaci a banki wajen cirar kudin da suka sha wahala wajen nemansu.

TRT Afrika