Yajin aikin NLC da TUC ya durkusar da harkoki a Nijeriya./Hoto:Reuters . Hoto/NLC

Kungiyar Kwadago ta Nigeria Labour Congress (NLC) da takwararta ta Trade Union Congress of Nigeria (TUC) sun janye yajin aikin da suka kwashe kwana biyu suna yi a fadin kasar.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne ranar Laraba da tsakar dare bayan wata ganawa da suka yi da Malam Nuhu Ribadu, Mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan Sha'anin Tsaro.

NLC da TUC sun ce sun janye yajin aikin ne bayan Malam Nuhu Ribadu ya tabbatar musu cewa za a hukunta mutanen da aka kama bisa zargin cin zarafin shugaban NLC Mr Joe Ajaero a jihar Imo da ke kudancin kasar.

Wannan shi ne karo na biyar da ake yajin aikin a bana a Nijeriya.

NLC da TUC sun ayyana tafiya yajin aikin tun tsakar daren Talatar da ta wuce, sakamakon wata takaddama da ta kaure tsakaninsu da gwamnatin jihar Imo kan zargin cin zarafin Mr Ajaero da 'yan sandan jihar suka yi, mako biyu da suka wuce.

Ranar 1 ga watan Nuwamba Mr Ajaero, tare da wasu shugabannin kungiyoyin kwadago, sun isa Owerri, babban birnin jihar Imo domin jagorantar wata zanga-zangar adawa da gwamnatin jihar bisa zargin keta hakkokin ma'aikata.

Sai dai gwamnan jihar, Hope Uzodinma, wanda a lokacin yake takarar neman wa'adi na biyu, ya zargi Mr Ajaero, dan asalin jihar ta Imo, da sanya siyasa a lamarin.

Wannan turka-turka ce ta janyo wasu da ake zargi 'yan sanda ne suka lakada wa shugaban na NLC duka lamarin da harzuka kungiyar ta tsunduma yajin aiki na kasa baki daya.

Yajin aikin ya durƙusar da ayyukan bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe da na tasoshin jiragen ruwa da jiragen ƙasa da fannin man fetur da ma dakatar da karatu a wasu makarantun gwamnati a wasu sassan ƙasar.

A makarantu irin su Jami'ar Bayero ta Kano har soke yin jarrabawar zangon karatu na farko da ɗalibai ke rubutawa aka yi a ranar Laraba.

Lamarin ya kuma jawo ɗaukewar wutar lantarki na baki dayan yinin Laraba a Nijeriya, inda hakan ya janyo wa mutane da dama, musamman masu harkokin kasuwanci asara.

TRT Afrika