Kungiyar Kwadago ta Nijeriya ta ce babu kasar duniya da ba ta bayar da tallafin ga 'ya'yanta don haka matakin Shugaba Tinubu na cire tallafin fetur rashin imani ne./Hoto: Reuters.

Gamayyar kungiyoyin kwadago na Nijeriya karkashin babbar Kungiyar Kwadago ta kasar, NLC, tana gudanar da zanga-zanga a yau Laraba domin bijire wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda karin farashin fetur.

Kungiyar kwadagon ta umarci dukkan rassanta da ke jihohi 36 da Abuja, babban birnin kasar sun tsunduma yajin aiki da zanga-zanga kan abin da suka kira "rashin imani" na gwamnatin Shugaba Tinubu.

Tuni aka soma zanga-zanga a jihohin kasar da suka hada da Legas, cibiyar kasuwancin Nijeriya da Kano, jiha mafi yawan jama'a a arewacin kasar.

'Yan kungiyar kwadago dauke da alluna da kwalayen da aka yi rubutu daban-daban a jikinsu, sun rika rera taken kungyar tare da kira ga gwamnatin kasar ta sauya aniyarta ta janye tattalin fetur.

Tun da farko, a sanarwar da ya fitar ranar Talata a daddare, shugaban NLC, Joe Ajaero ya karyata rahotannin da ke cewa sun janye daga zanga-zangar yana mai bayyana su a matsayin "na masu mugun nufi."

“Muna so mu sanar da dukkan 'yan Nijeriya cewa yanzu muka gama taro da Gwamnatin Tarayya inda muka so su saurari bukatun al'uuma da ma'aikatan Nijeriya.

"Sakamakon taron namu na yau bai sauya komai ba da kuma kudurinmu na soma abin da muka kuduri aniyar yi gobe domin 'yan Nijeriya da kuma bukatar ma'aikata da ta 'yan kasar," in ji sanarwar.

A watan Mayu ne Shugaba Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a Nijeriya yana mai cewa hakan ba ya amfanar galibin 'yan kasar sai wasu tsirarun 'yan damfara.

Sai dai hakan ya sa farashin fetur ya tashi inda ya kai fiye da naira 600, lamarin da ya shafi farashin kusan komai a Nijeriya.

A makon nan shugaban ya ce kasar ta adana fiye da naira tiriliyan daya wata daya bayan janye tallafin, inda ya sha alwashin yin amfani da kudin wurin inganta rayuwar 'yan kasar kai-tsaye.

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta fitar da sanarwa da ke cewa ba za ta lamunci zanga-zangar da za ta haifar da rikici ba sanna ta kara jami'an tsaro a sassan kasar.

TRT Afrika