Ma'aikata daga kowane bangare a Nijeriya sun fara yajin aiki saboda tsadar rayuwa sanadin cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi, inda suka yi barazanar za su "durkusar" da al'amura a kasar da ta fi kowace karfin tattalin arziki a Afirka, idan gwamnati ta kasa biya musu bukatunsu.
Mambobin Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) sun fara yajin "aikin gargadi" a ranar Talata, wannan yajin aikin shi ne na biyu a fiye da wata daya.
Sun gana a makon jiya kuma sun yi korafin cewa matakin da gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta dauka na cire tallafin man fetur "ya jawo masifa kan ma'aikatan Nijeriya da talakawa."
Wani yunkurin fasa yajin aiki bai yi nasara ba ranar Litinin da yamma, bayan da shugabannin kungiyar NLC suka ki halartar wata ganawa da Ma'aikatar Kwadagon kasar ta kira su.
Yajin aikin ma'aikata daga kowane bangare ciki har ma'aikatan wutar lantarki da na kiwon lafiya, ana saran zai tsayar da al'amura a kasar wadda ta fi kowace karfin tattalin arziki a Afirka, da ma kuma tattalin arziki kasar yana tafiyar hawainiya saboda raguwar kudin shigar gwamnati da matsalar satar danyen man fetur.
Shugaban Kungiyar Kwadagon Joe Ajaero ya ce "za a tsayar da duka al'amura a kasar" a cikin mako biyu, idan har gwamnati ba ta biya bukatun ma'aikata ba ciki har da karin albashi.
Shugaba Tinubu, wanda aka rantsar da shi a watan Mayu, ya ce zai bunkasa tattalin arzikin Nijeriya wanda hakan ne ya sa shi daukar wasu tsauraran matakai, wadanda ya ce za su sa a rage kashe kudi da farfado da darajar naira da kuma jawo masu zuba jari.
Amma wadannan matakai sun jawo tsanani ga miliyoyin 'yan kasar, inda masu sukar gwamnatin Tinubu suke cewa ba shi da zafin nama wajen fito da tsare-tsaren rage radadin matakan da ya dauka.
Bayan ya cire tallafin man fetur a ranar farkonsa ta kama aiki, farashin man fetur ya ninka fiye da sau biyu wanda hakan ya sa farashin sauran kayayyaki su ma suka tashi.
Haka zalika matakin gwamnatin na karya darajar naira ya kara sa farashin kayayyakin abinci tashi.
Gwamnatin Nijeriya ta dauki wasu matakai don rage halin matsin da aka shiga ciki har da ware dala miliyan 5.5 ga jihohi a matsayin kyauta da kuma rance.
Sai dai ma'aikatan sun ce wannan bai wadatar ba, saboda har yanzu albashinsu bai sauya ba.
Ma'aikata da dama ba sa iya biyan kudin motar zuwa wajen aiki, a cewar Ajaero yayin da yake magana kan "matsanancin halin yunwa da ake fuskanta a duk fadin kasar."
Gwamnatin a nata bangaren ta ce yajin aikin zai kara sa al'amura su tabarbare ne a Nijeriya kuma ta bukaci a ba ta karin lokaci don warware matsalar.
"Bai kamata mu yi wannan a daidai lokacin da ake cikin yajin aiki ba," in ji Ministan Kwadago Simon Lalong.