A cikin kwana 21 da suka ba ta bayan yajin aikin gargadi na kwana biyu da suka yi a ranakun 5 da 6 ga watan Satumba. Hoto: NLC

Kungiyoyin ƙwadago na Nijeriya syn sanar da cewa za su tafi wani yajin aikin na duk ƙasa daga ranar Talata 3 ga watan Oktoban 2023.

Kungiyoyin na TUC da NLC sun fadi matakin ne a wata sanarwa da suka fitar a ranar Talata 26 ga watan Satumba, bayan wani taro da shugabannin kungiyoyin suka yi a tsakaninsu.

Shugabannin kungiyoyin sun ce sun yanke hukuncin tafiya yajin aikin ne saboda gaza girmama yarjejeniyoyinsu da gwamnati ta yi, da suka cimma kan batun cire tallafin man fetur.

A wasu taruka da kwamitocin ƙoli na ƙungiyoyin NLC da TUC suka yi, sun yi duba na tsanaki kan yanayin da ake ciki a ƙasar na wahalhalu da jama’a ke sha a faɗin ƙasar, tare da yin Allah wadai da halin da tsadar fetur ta jefa ƴan Nijeriya, in ji sanarwar.

Kungiyoyin sun kuma tattauna kan ƙin amincewar gwamnati wajen tattaunawa don samo mafita kan matsalar da ake ciki, a cikin kwana 21 da suka ba ta bayan yajin aikin gargadi na kwana biyu da suka yi a ranakun 5 da 6 ga watan Satumba.

NLC da TUC sun bayyana wasu dalilai 11 da suka sa suka yanke hukuncin tafiya sabon yajin aikin, kamar haka:

1. Kungiyar ƙwadago da gwamnati duka sun yarda cewa ana shan wahala a ƙsar, kuma ana fama da yunwa da talauci sakamakon tsadar da man fetur ya yi, lamarin da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa don magance shi.

2. Gwamnati ta yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyanta inda ta nuna halin ko oho wajen cire ƴan Nijeriya da ma'aikata daga halin tsananin talauci da wahalar da suke ciki.

3. Gwamnatin tarayya tana ci gaba da ƙin mayar da hankali kan bin duk wasu hanyoyi na tattaunawa da kungiyoyin ƙwadago don lalubo bakin zaren yadda za a ceci ƴan Nijeriya daga yunwa da wahalhalu da tsadar man fetur ta jawo a ƙasar, wacce gwamnatin ce ta jawo hakan.

4. Baya ga ci gaba da yin biris da gwamnatin ke yi wajen magance wahalar da ake sha a ƙasar, tana kuma nuna rashin tausayi kan halin da mutane ke ciki.

5. Gwamnatin tarayya ba ta yi wata hoɓɓasa ba don ganin ta cika buƙatun ma'aikatan Nijeriya da al'ummar ƙasar kamar yadda aka cimma a yarjejeniyoyin da aka cimma da ita na ceto tattalin arziki da kare ma'aikata da 'yan ƙasar daga shan wahala.

6. Wa'adin da ƙungiyoyin ƙwadagon suka bayar ya ƙare ba tare da gwamnati ta ɗauki mataki ba.

7. Kungiyoyin ma’aikata na ci gaba da fuskantar barazana daga gwamnati ta hanyar amfani da karfin ‘yan sanda da gwamnati ke yi a kansu.

8. Kungiyar Ma’aikatan Sufurin (NURTW) na ci gaba da zama karkashin mamayar gwamnati ta hanyar amfani da ‘yan sanda da suka kanainaye shugabancin NURTW

9. Kungiyar Masu Bayar da Ayyukan Sufurin Hanya ta Kasa (RTEAN) na ci gaba da zama karkashin mamayar gwamnatin jihar Legas inda aka yi watsi da umarnin kotuna da dokoki.

10. ’Yan sanda sun kashe tare da jikkata ‘yan kwadago da dama a lokacin da suke kan hanyar koma wa hedikwatarsu da ke Abuja.

11. Gwamnati na ci gaba da ɓata suna da ɗaukar nauyin gangamin baƙanta shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa da na ma’aikata a shafukan sada zumunta na yanar gizo, inda suke amfani da ƙarfin tuwo da na kudade, maimakon su mayar da hankali wajen raba jama’a da wahalhalu.

A hannu guda kuma, gamayyar kungiyoyin ƙwadago da ma’aikata sun cimma wadannan abubuwa a zaman da suka yi:

1. Albarkacin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai da bayyana matakinmu na ‘yantacciyar Nijeriya, mu dauki kaddararmu da kanmu tare da kubutar da kasarmu.

2. Za mu fara yajin aikin sai baba-ta-gani a dukkan fadin kasar daga 12 daren ranar Talata, 3 ga Oktoban 2023.

3. Za mu umarni dukkan ma’aikata a Nijeriya su janye ayyukansu daga ko ina tun daga ranar 3 ga Oktoba.

4. Umartar dukkan rassa da shugabancin jihohi da su gaggauta fara zaburarwa don fita zanga-zanga a kan tituna har sai gwamnati ta biya bukatunmu.

5. Za a kuma bukaci dukkan ‘yan Nijeriya masu kishi da su hada hannu waje guda don taimaka wa wannan gwamnati don ta sanya al’umma a gaba a cikin manufofi da shirye-shiryenta.

TRT Afrika