Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar NLC da TUC su janye yajin aikin da suke shirin farawa a yau Talata a fadin kasar.
Tun a makon da jiya ne ƙungiyoyin suka ayyana tafiya yajin aiki daga ranar Talata 14 ga Nuwamban 2023.
Sai kuma a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba ƙungiyoyin biyu suka sake yin kira ga ma’aikata a fadin kasar cewa su ajiye ayyukan gwamnati don fara yajin aiki, a daidai lokacin da rikicin da suke yi da gwamnatin jihar Imo ke shafar ƙasar baki ɗaya.
Sai dai a wata sanarwa da mai taimaka wa Lateef Fagbemi, Ministan Shari'a na ƙasar kan watsa labarai, Kamarudeen Ogundele ya fitar a ranar Litinin da maraice, ya tuna wa ƙungiyoyin NLC da TUC batun wani umarni da kotu ta bayar na hana su tafiya yajin aikin.
"Muna so mu tunatar da Kungiyar Kwadago ta Ma'aikata da Kungiyar Kwadago ta 'Yan Kasuwa na Nijeriya cewa akwai wani umarni da kotu ta bayar na dakatar da su daga shiga yajin aikin,” in ji sanarwar.
"Shugaban Kotun Masana’antu ta Nijeriya Mai Shari’a B. B. Kanyip ne ya bayar da umarnin na wucin gadi a ranar 10 ga watan Nuwamba.
"Kotu ta bai wa ƙungiyoyin umarni, don haka, dole ne su bi umarnin da kotun ta bayar tare da miƙa kansu ga hukuma. Duk wani mataki da aka dauka wanda ya saba wa umarnin zai zama tamkar wulakanci ne ga kotu," in ji sanarwar.
Kazalika gwamnatin tarayya ta yi kira ga ƙungiyoyin ƙadagon da ma ma'aikata cewa "su girmama umarnin kotu tare da bin doka da oda."
"Muna kira ga ma'aikata da su je aiki, kuma ka da su ji tsoron komai saboda an tabbatar da tsaron su kuma za a kare su a cikin tsarin doka."
Shugabannin ƙungiyoyin sun cimma matsayar tafiya yajin aikin ne a wani taro da suka yi a Abuja a ranar Talatar makon da ya wuce, inda suka ce tuni suka fara haɗo kan mambobinsu da abokan hulɗarsu a fadin ƙasar don tafiya yajin aikin ba tare da ɓata lokaci ba.
Kungiyar kwadagon ta ɗauki matakin tafiya yajin aikin ne sakamakon “cin zarafin” shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, da suke zargin rundunar ƴan sanda da yi a Jihar Imo, mako biyu da suka wuce.