Kungiyar likitoci ta Nijeriya ta ce a kowanne mako akalla likitoci hamsin na ficewa daga kasar./Hoto: OTHER

Kungiyar likotoci masu neman kwarewa ta Nijeriya ta soma yajin aiki na sai abin da hali ya yi ranar Laraba.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce ta tsunduma yajin aiki don neman gwamnati ta kara wa mambobinta albashi da alawus-alawus.

Kazalika kungiyar ta yi korafi game da yadda aka tsame wasu daga cikin mambobinta daga kudin ariyas da ake bayarwa tana mai yin kira ga gwamnati ta biya su kudin.

Kungiyar likitoci ta Nijeriya ta ce a kowanne mako likitoci hamsin na ficewa daga kasar.

Yajin aikin likitoci na shafar harkokin kiwon lafiya musamman a asibitocin gwamnati.

A ranar Litinin ne shugaban majalisar wakilan Nijeriya Tajudeen Abbas ya yi kokarin rarrashin kungiyar likotocin don kada ta shiga yajin aikin amma ta ki yarda.

Ranar 5 ga watan nan na Yuli ne kungiyar likitocin ta bai wa gwamnatin kasar wa'adin mako biyu don ta biya mata bukatunta idan ba haka ba ta shiga yajin aiki.

TRT Afrika