Hukumar kula da masu buƙata ta musamman a Nijeriya (NCPWD) ta bayyana shirinta na tattara bayanan masu larura ta muasamman a ƙasar ta hanyar intanet.
Shugaban hukumar, Ayuba Gufwan ne ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin a lokacin tunawa da ranar masu buƙata ta musamman ta duniya (IDPDs).
Gufwan ya ce shirin, wanda hukumarsa za ta yi da haɗin gwiwar hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), zai tatara cikakkun bayanai kan masu buƙata ta musamman a ƙasar.
“Wannan ƙidayar ta intanet za ta yi amfani sama da akwati 760 wajen tattara bayanan mutane da ke da buƙata ta musamman ciki har da jinsi da shekaru da nau’in larura da kuma sauran muhimman bayanai,” in ji shi.
Ya bayyana cewa bayanan za su yi amfani wajen yanke shawarwari kan tsare-tsare da kasafin kuɗi da kuma tsara shirye-shirye don tallafa wa masu buƙata a Nijeriya.
Muhimmancin ƙidaya ta intanet
Gufwan ya bayyana cewa ana sa ran ƙidayar za ta sa a iya samun daidaito wajen ƙiyasta yawan mutane masu buƙata ta musamman a ƙasar, waɗanda a halin yanzu ana ganin sun kai mutum miliyan 35.
Ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da ƙungiyoyin fararen-hula da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa su tallafa wa shirin domin tabbatar da nasararsa.
Babban mai bai wa shugabn ƙasa shawara kan masu buƙata ta musamman, Mohammed Isa, ya ce gwamnatin tana amfani da hukumar don ƙara wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa masu larura ta musamman.