Gwamnatin Nijeriya ta zargi wani kamfanin ƙasar China da yunƙurin ƙwace kadarorinta a ƙasashen ƙetare ciki har da jiragen Shugaban Ƙasa, kamar yadda kakakin shugaban ƙasar ya bayyana a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasar, Bayo Onanuga, ya ce Kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Ltd yana amfani da “hanyar da ba ta dace ba” wajen ƙoƙarin ƙwace kadarorin gwamnatin Nijeriya, duk da cewa ba shi da wata alaƙa ta kwangila da gwamnatin tarayyar.
Kamfanin Zhongshan bai mayar da martani ba nan-take.
Taƙaddamar dai ta samo asali ne daga wata kwangilar da Zhongshan ya ƙulla da jihar Ogun ta kudu maso yammacin Nijeriya a shekarar 2007, ta samar da yankin kasuwanci marar shinge, wanda aka soke a shekarar 2015.
'Babu ƙaƙƙarfar hujja'
Onanuga ya ce lokacin da aka soke kwantiragin jihar Ogun a shekarar 2015, abin da Zhongshan ya yi na aikin bai wuce gina katanga ba a filin da aka keɓe domin gina yankin kasuwanci marar shingen.
“Zhongshan ba shi da ƙwaƙƙwarar hujjar da zai buƙaci gwamnatin jihar Ogun ta biya shi bisa hujjar kwangilar da aka ƙulla tsakanin kamfanin da gwamnatin jihar a shekarar 2007 don gina yankin kasuwanci marar shinge,” in ji Onanuga.
Gwamnatin Nijeriyar dai ta ce ba ta cikin wannan kwangilar, kuma Zhongshan ya gabatar da wasu hujjoji da ba daidai ba a gaban kotuna a Birtaniya, da Amurka, da kuma Faransa, inda kotu ta ce a biya shi dala miliyan 60 a matsayin diyya.
Nijeriya ta ƙi biyan waɗannan kuɗaɗe, in ji Onanuga.
Kadarorin da ba su da kariya
Onanuga ya ce, Zhongshan ya samu umarni biyu daga wata kotun Faransa a watan Maris da Agusta na ƙwace kadarorin Nijeriya, ciki har da jiragen Shugaban Ƙasa da ake kula da su a Faransa.
Ya ce waɗannan kadarorin ba su da kariya daga ayyukan shari'a na ƙasashen waje.
Gwamnatin Nijeriya na aiki tare da jihar Ogun domin shawo kan rikicin da kuma kare kadarorin ƙasar daga ƙwace, in ji Onanuga.