Hukumomi a Nijeriya sun ce sun yi nasarar dawo da 'yan kasar 108 da suka makale a Jamhuriyar Nijar zuwa gida a ranar Talata.
Gwamnatin Tarayya Nijeriya tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya, IOM ne suka dauki nauyin dawo da mutanen gida.
A wata sanarwa da jami'in Shiyyar Kudu maso Yamma na hukumar Kula da 'yan Gudun Hijira ta Nijeriiya (NCFRMI) Mista Alexander Oturu ya fitar a ranar Talata a Abuja, ya ce tuni aka mika 'yan kasar da suka kasance bakin-haure a Jamhuriyar Nijar zuwa ga sansanin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas.
Jimillar maza 32 da mata 29 da yara 44 da kuma jarirai 3 ne a cikin mutane 108 da aka yi nasarar dawo da su kasarsu a cikin wani jirgi da hukumar IOM ta yi hayarsa daga Jamhuriyar Nijar, a cewar Mista Alexander Oturu.
''Za a sanya su cikin shirye-shiryen gwamnati da kuma hukumar kula da shige-da-fice ta Majalisar Dinkin Duniya karkashin tsarin shugaban kasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu," in ji shi.
Jami’an hukumar NCFRMI da hukumar shige-da-fice ta kasa NIS sun tantance bakin-hauren, kazalika jami’an kiwon lafiya na filin jiragen sama da Cibiyar Kula da 'yan Gudun Hijira (Migrants Resource Centre) da Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA duk sun ba da gudumawa wajen tabbatar da lafiyar mutanen.