Kamfanin Orano na Faransa, mai haƙar makamashin uranium a ƙasar Nijar ya sanar da cewa gwamnatin Nijar ta ƙwace masa lasisin haƙar uranium a tashar ma'adanai ta yankin Imouraren da ke arewacin ƙasar.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Alhamis, ya ce ya yi na’am da matakin na gwamnatin mulki soji ta Nijar ta ɗauka, duk da yunƙurinsa na fara aiki a sabuwar tashar haƙar ma'adanan.
Kamfanin Orano S.A, ya kuma ce yana da haƙƙin ƙalubalantar matakin a gaban kotunan da suka dace, ko na cikin ƙasa ko kuma ƙasa-da-ƙasa.
A kwanan nan dai bayanai sun ce kamfanin ya ɗan soma aiki a sabuwar tashar, bayan da gwamnatin Nijar ta ɗibar masa wa’adin zuwa ranar 19 ga watan Yunin 2024, na ya fara aikin ko kuma a ƙwace masa lasisi.
Da ma dai gwamnatin soji ta Nijar ta sha alwashin sake bitar yarjejeniyar haƙar ma'adanai a ƙasar, kuma ma'aikatar ma'adanai ce ta ba wa kamfanin wa'adin fara aikin.
Wasu ‘yan Nijar da dama na ganin matakin da gwamnati ta ɗauka, yana da nasaba da sabuwar hulɗar da ƙasar ta ƙulla da Rasha, da ma Iran, kan batun makamashi.
Kamfanin na Orano yana sarrafa ma'adanin uranium ne don samar da makamashin nukiliya, kuma mahaƙar da ke Imouraren tana cikin wuraren haƙar uranium mafi girma a duniya.
Mahaƙar Imouraren da ke arewacin Nijar tana da ƙiyasin tan 200,000 na ma'adanin, wanda ake sarrafawa don samar da wutar lantarki ta fasahar nukiya, da kuma makamin ƙare-dangi na nukiliya.
Tun a shekarar 2015 ne ya kamata a fara aiki a mahaƙar Imouraren, amma sai aka dakatar sakamakon faɗuwar farashin uranium a kasuwar duniya, bayan da aka samu bala'in nukiliya a ƙasar Japan a 2011.
Kamfanin na Faransa yana aiki a Nijar tun shekarar 1971, duk da cewa ya rufe mahaƙar uranium ta Arkokan a shekarar 2021. Amma har yanzu Orano yana aiki a wata mahaƙar uranium a arewacin ƙasar da ke Arlit.