An sanar da Birgediya Janar A. Tchiani a matsayin sabon shugaban kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Mohamed Bazoum. Hoto/Reuters

Gwamnatin mulkin soji ta Jamhuriyyar Nijar ta sanar da sake bude iyakokinta da kasashe biyar tare da nada sabbin gwamnoni na soji a jihohi takwas na kasar.

Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a makon jiya ne aka rufe iyakokin kasar da Nijeriya, Mali, Burkina Faso, Libya, Aljeriya da kuma Chadi, kamar yadda sojojin suka sanar a talabijin.

“Iyakoki na kan tudu da na sama da Aljeriya da Burkina Faso da Libya da Mali da Chadi an bude su daga yau (Talata)”, in ji sojojin.

Sai dai sojojin ba su ce komai ba kan batun bude iyakar Nijar da Nijeriya.

Haka kuma shugaban mulkin soji na Nijar Birgediya Janar A. Tchiani a ranar Talata ya saka hannu a kan wata dokar soji wadda ta nada gwamnoni a kasar.

Dokar ta nada manyan jami’an tsaron kasar takwas a matsayin gwamnoni. Sabbin gwamnonin sun hada da:

Agadez - Birgediya Janar Ibro Boulama

Dosso - Birgediya Janar Iro Oumarou

Diffa - Birgediya Janar Ibrahim Bagadoma

Yamai - Birgediya Janar Abdou Assouman Harouna

Tahoua – Manjo Kanal Oumarou Tawayé

Maradi – Sufeto Janar na ‘yan sanda Issoufou Mamane

Tillabery – Laftanar Kanar Maïna Boukar

Zinder - Kanal EF Labo Issoufou

Fargabar karancin albasa a Ghana

A gefe daya, ‘yan kasuwa a Ghana na cikin fargaba sakamakon rade-radin da ake yi cewa za a samu karancin albasa bayan da kungiyar ECOWAS ta saka takunkumi kan Nijar sakamakon juyin mulki.

A 2021, Nijar ta samar da tan miliyan 1.35 na albasa, kamar yadda hukumomi suka bayyana. Hoto/AP

Ghana na shigar da kusan kashi 70 cikin 100 na albasar da take amfani da ita daga Nijar, kamar yadda wani jami’i na kungiyar masu sayar da albasa ta kasar ya bayyana.

“Idan iyakar Nijar ta ci gaba da zama a rufe tsawon lokaci, hakan zai shafi kasuwancin albasarmu matuka. Hakan kuma zai sa farashinta ya tashi sosai,” in ji Ali Umar, wakili na masu sayar da albasa a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Ghana.

Nijeriya ce ke samar da kashi 20 cikin 100 na albasar da ake amfani da ita a Ghana sai Burkina Faso ta samar da kashi biyar, kamar yadda Umar ya bayyana.

Ita kuma kasar ta Ghana tana samar da kashi biyar ne kacal cikin 100 na albasar da ake amfani da ita a kasar.

TRT Afrika